RIKICIN SIYASA: Dan'majen Gwandu Ya Gargadi Chika Malami

Chika Malami Ba Zai iya kawar da Hankalin APC da Gwamna Nasir Idris (Kauran Gwandu) Daga Ayukkan Alherin Da Suke yi

A matsayina na ɗan ƙasa mai kishin jihar Kebbi, ya zama dole in yi magana kan wannan hayaniya da Abubakar Malami SAN yake ƙoƙarin tayarwa. 

Abin da muka gani kwanakin nan ba shugabanci ba ne, sai dai yunƙurin neman asan da shi a siyasa. Idan mutum bai da abin rasawa, zai iya fasawa kowa ya rasa, sannan ya dinga zargin an Kai masa hari. Wannan ne abinda Chika Malami ke kokarin yi yanzu.

A maimaikon ya fuskanci matsalolinsa da kariyar mutuncin sa, sai ya fake da ƙirƙirar rikici don nuna wai yana da magoya baya. 

Amma mutanen Kebbi sun san abinda sukeyi. Gaskiya a fili take: yana fuskantar wasu manyan shari’o’i a EFCC a kan yadda ya gudanar da ofishinsa a lokacin mulkinsa. Amma maimakon ya je ya kare kansa, sai ya zabi wasa da hankalin al'umma da ƙarairayi kai ka ce shiri ne na wasan kwaikwayo.

 Burinsa na zama gwamna ba ɓoyayyen abu ba ne, musamman yadda ya yi gini a kan ƙarya, ta hanyar raba kan al'umma wanda hakan ba zai yi tasiri a Kebbi ba.

Mutanen Kebbi sun riga sun yanke shawara. Sun tsaya tsayin daka tare da Dr. Nasir Idris (Kauran Gwandu) da kuma Mai Girma Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu, GCFR. 

Jam'iyar APC ta sami Mulki ne da yardar jama’a, ba da magudi ba, kuma ba za a anshe wannan mulkin da ƙarya da munafincin siyasa ba.

 A duk faɗin Kebbi yau, daga birane zuwa ƙauyuka, labari ɗaya ake ji: mutane suna ganin cigaba a fili, suna kuma shaida cewa sabon zamani ya zo musu.

Hanyoyin da ake ginawa, makarantu da ake gyarawa, aikin lafiya da ake ingantawa wanda kai tsaye yake taɓa rayuwar talakawa, da shirye-shiryen tallafa wa al’umma don fitar da al'umma daga talauci, da shirye-shiryen bunƙasa matasa — waɗannan su ne manufofi na shugabanci na gaskiya da Gwamnatin APC Ke aiwatarwa a matakin jiha da kasa baki daya.

 A karo na farko cikin shekaru da dama, mutanen Kebbi na iya cewa suna ganin manyan ayyuka da suka shafi rayuwar kowa a ko’ina cikin jihar.

 Wannan ba magana ba ce kawai, a zahirance lamarin yake, domin gani ya kori ji.

Idan aka kwatanta wannan da dabarun Chika Malami, sai a ga cewa abin nasa wauta ce. Yadda ya umarci motocin rakiyarsa su tsaya a gaban hedikwatar APC da ke da tazarar ɗan ƙanƙanin ƙafa daga gidansa tamkar wasan kwaikwayo. Burinsa shi ne ya tada rikici, ya tsokani magoya bayan APC, sannan ya yi kuka a matsayin wanda aka zalunta don neman tausayi daga ƙasashen waje. 

Amma wannan zamani ne na da komai a zahiri yake. Mutane suna ganin gaskiya nan take. Bidiyo, hotuna da shaidun gani-da-ido suna bayyana gaskiya a lokacin da abin ke faruwa. Ba wata diramar da ya shirya da zai yaudari mutane yanzu.
Abu mafi ban takaici shi ne rashin godiyar Allah. APC ce ta ba Chika Malami komai. Ita ce ta amince da shi ta ba shi muƙamin Babban Lauyan Tarayya, ɗaya daga cikin manyan muƙamai a Nijeriya. Ita ce ta ba shi dandali, iko, da suna a ƙasa baki ɗaya. Amma me ya saka mata da shi? Maimaikon godiya da biyayya, sai ya juyo ya yi wa gidan da suka raina shi butulci. Ya zaɓi butulci maimakon amana, ya zaɓi yaudara maimakon halasci, ya zaɓi ƙarya a madadin gaskiya.

Duk da haka babu abin da za mu ce sai mu gode wa Allah domin mutanen Kebbi sun riga da sun farga. Sun san wanda ke yi musu aiki don Allah don kuma cigaban jihar Kebbi. Sun san APC na da tare da su. Sun san Dr. Nasir Idris, Kauran Gwandu, shugaba ne mai mayar da hankali kan ilimi, cigaba, da mutunta al'umma. Sun san Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu, GCFR, na da niyar gina Nijeriya. Wannan ne ya sa mutanen Kebbi suka tsaya daram da APC a matakin jiha da ƙasa. Ba wata ƙarya da za ta girgiza musu imaninsu.

Ina sanar da duniya, ta ji wannan a fili: APC da Dr. Nasir Idris ba za su shiga cikin batutuwan banza ba. Sun fi girmi haka. Shugabanci ba wai magana ba ne, aiki ne — kuma aikin ne mutanen Kebbi ke gani yanzu haka.

Ga Chika Malami, shawarar da zan ba ka mai sauƙi ce: Ka daina ƙona gidan da ya raine ka. Ka daina haifar da ruɗani don neman a tausaya maka. Ka girmama zaɓin mutanen Kebbi. Ka fuskanci matsalolinka da ƙarfin zuciya, idan har kana ƙaunar Kebbi, ka goyi bayan cigaban da mutanen ke ji da gani a yau. Siyasa ba wai yunƙuri da rikici ba ne, hidima ce.

Kebbi ta ci gaba. Mutanen sun zaɓi cigaba maimakon akasinsa, sun zaɓi mutanen da za su hidimta musu maimakon 'yan son rai, sun zaɓi haɗin kai maimakon ruɗani. Sun tsaya tsayin daka tare da APC, da Gwamna Nasir Idris, da Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu. Wannan shi ne gaskiyar da babu wani abu da zai canza ta.

Kamar yadda na fada, Ina kara jaddadawa cewa , IN SHA ALLAH, babu gurbi a ASO ROCK da FADAR GWAMNATIN JIHAR KEBBI a zaben 2027.
 Engr. Ahmed Umar Farouk , FNSE, MCOREN, NPOM
(Danmajen Gwandu / Gamjin Kabi)

Post a Comment

0 Comments