Tarihin Dan'Majen Gwandu (Kashi Na 8)
ASAN MUTUM; ASAN HALIN SA; ASAN AIKIN SA : SHARHI AKAN RAYUWAR DAN'MAJEN GWANDU
( Kashi Na 8)
NASARORIN DAN'MAJEN GWANDU A HUKUMAR 'NAMA' A MATSAYIN SA NA 'MD'
Daga Ahmed Umar
Sanin mutum da sanin halin sa da kuma sanin aiki sa, sune ma'aunin hankali da mutane ya kamata suyi la'akari da su wajen ma'amala ta yaro da uban-gida da kuma wajen zaben shugabanni.
A wannan kashi na 8, akan sharhin tarihin Injiniya Ahmad Umar Farouk (Dan Majen Gwandu, Gamjin Kabi) Kuma Shugaban Hukumar Kula da Sararin Samaniya na Nijeriya (watau MD, Nigeria Airspace Management Agency 'NAMA') zamuyi takaitaccen bayani akan nasarorin da ya samu a hukumar kula da sararin samaniya ta Nijeriya (watau Nigeria Airspace Management Agency 'NAMA')
1-WANE NE INJINIYA AHMED UMAR FAROUK (DAN MAJEN GWANDU)? kashi na 8:
Injiniya Ahmad Umar Farouk (Dan'Majen Gwandu) ya sami nasaran kawo sauye sauye da dama a filayen sauka da tashin jiragen sama dake Nijeriya ta hanyar canza tsaffin na'urori da maye gurbin su da na'urorin zamani.
Wannan sauye sauyen sun taimaka sosai wajen rage hatsarin jiragen sama a Nijeriya.
Ga kadan daga cikin wayannan sauye sauye da Dan'Majen Gwandu ya jagoranta a hukumar NAMA:
- Injiniya Ahmad Umar Farouk ya sami nasaran canza tsaffin na'orori a dukkan filayen jiragen sama dake Nijeriya ta hanyar kawo wata na'ora da ake kira 'Doppler Very High Frequency Omni Directional Radio Range 'DVOR' da kuma wata na'ora da ake kira 'VHF Communication ' wayannan na'urorin sun taimaka wajen inganta safaran jiragen sama a Nijeriya
- Ya samar da na'urorin taimakawa saukan jiragen sama (Instrument Landing System) a filayen jiragen sama da dama a Nijeriya
- Dan'Majen Gwandu ya sami nasaran kawo na'uran da ake kira 'High Power Stand Alone Upper Air Communication System (RCAG)' da ya taimaka sosai wajen saukaka sadarwa tsakanin matukin jirgin sama da ma'aikatan dake filin jirgi
- Dan'Majen Gwandu ya kuma samar da na'urorin da ake kira 'VHF Stand Alone for Aerodrome and Approch Radio Communication System' shima wannan na'urane na zamani da ke inganta sadarwa da matukin jirgin sama a duk inda yake a duniya
- Dan'Majen Gwandu ya samar da na'uran da ake kira 'IP based PABX' dake muhinmanci sosai a filin jiragen sama
- Dan'Majen Gwandu ya samar da manyan na'urorin solar domin tabbatar da wuta a kodayaushe a filayen jiragen sama a Nijeriya
- Dan'Majen Gwandu ya samar da na'uran da ake kira 'Surface Movement Radar(SMR) da sauran su.
Wayannan nasarori sun taimaka wajen rage afkuwan hadarin jiragen sama a Nijeriya.
YADDA JAHAR KEBBI TA ANFANA DA MATSAYIN DAN'MAJEN GWANDU A HUKUMAR NAMA
- Dan'Majen Gwandu yayi anfani da wannan damar wajen samarwa dinbim matasan jihar Kebbi aiki a hukumar NAMA dama Ma'aikatar sufirin jiragen sama (Ministry of Aviation)
- Dan'Majen Gwandu yayi anfani da wannan damar wajen inganta filin jirgi sama na Sir Ahmadu Bello International Airport, Birnin Kebbi da na'urorin zamani, wannan ya sa Sir Ahmadu Bello International Airport Birnin Kebbi yanzu yana cikin manyan filaye jirgin sama a Nijeriya
- Dan'Majen Gwandu ya kirkiro da gidauniya a sihirce Inda yake taimakawa bayin Allah dare da rana
A LOKACIN MULKIN SA, SHUGABA MUHAMMADU BUHARI, DA WASU KUNGIYOYI DA DAMA SUN KARRAMA DAN'MAJEN GWANDU BISA WAYANNAN NASARORI DA YA SAMU...... Abiyo mu a Kashi na 9 domin karin bayani.
Mu hadu a kashi na 9 : A kashi na gaba watau Kashi na 9, zamuyi karin bayani akan yadda lokacin mulkin Buhari aka karrama Dan'Majen Gwandu da Kuma yadda wasu kungiyoyi suma suka karrama shi bisa iya aiki da shugabanci.
2- MENE NE HALAYAN INJINIYA AHMED UMAR FAROUK (DAN MAJEN GWANDU)?
Gaskiya, rikon amana da so da kaunar jama'a sune halayar Dan'Majen Gwandu
3- MENE NE AYUKKAN INJINIYA AHMED UMAR FAROUK (DAN MAJEN GWANDU) ?
Bautan Allah, Alheri, Kyauta, da Tausayin bayin Allah sune ayukkan Dan Majen Gwandu
____________________
Ahmed Umar
ahmadugamji@gmail.com
07038182929
Post a Comment
0 Comments