Gwamnatin Jama'a A Dandi
SHUGABAN KARAMAR HUKUMAR DANDI DR. MANSUR ISAH YA KAMMALA SAURAREN AYUKKAN DA JAMA'AR DANDI KE BUKATA DAGA GWAMNATI
-----Yayi alkawalin Daukan Malaman Makaranta 100
____Ya Bada Naira Miliyan 10 (N10million) cikin aljihun sa domin aikin kwamiti
A ranar Attanin 20/5/2025 Shugaban Karamar Hukumar Dandi Dr Mansur Isah ya kammala zagayen dukkan mazabu 11 dake karkashin hukumar Mulki ta Dandi domin sauraren ra'ayoyin jama'a da Kuma ayukkan da suke bukata daga Gwamnati.
Wannan wani hikima ne da Dr. Mansur ya kirkiro sabanin yadda ake gudanar da mulkin jama'a a baya inda haka Kawai shugaban Karamar hukuma zai yanke shawaran aikin da zaiyiwa jama'a ba tare da yaji shawaran su ba, kuma ko suna da ra'ayi akan aiki ko basu da ra'ayi.
Kaucewa wannan tsohon tsarin ne yasa Shugaban Karamar Hukumar Dandi, Dr. Mansur Isah ya kirkiro da wannan sabon tsari na sa jama'a gaba su fadi irin ayukkan da suke so domin ci gaban su.
Yanzu dai an kammala sauraren ra'ayoyin jama'a a dukkan wards 11 da suka hada da Gezah, Shiko, Dolekaina, Maigwaza, Fana, Kyangakwai, Kwakkwaba, Banizumbu, Kamba-Kamba, Maihausawa da Buma.
MATSALOLIN DA SUKA FI CIWA AL'UMMAR DANDI TUWO A KWARYA
A zagayen da Dr. Mansur ya gudanar an gano matsaloli sama da 100 dake damun mutanen Dandi, amma 5 mafi girma da muhinmanci sune:
1- Matsalar hanyoyi
2- Matsalar rashin aiki
3- Matsalar rashin Malamai a makaranta dama rashin isassun azuzuwa
4- Matsalar asibiti da wadattatun ma'aikatan Asibiti
5- Matsalar ruwan sha Mai tsabta da wutan Lantarki da sauran su.
DR. MANSUR YA FARA AIWATAR DA BUKATUN AL'UMMAN DANDI
Dr. Mansur ya fara aiwatar da wasu daga cikin bukatun da al'umma Dandi suka bayar Inda ya fara tuntubar Gwamnatin Jiha da wasu hukomomi tare da samun tabbacin za a fara aikin gina hanyoyi da dama a Dandi.
Dr. Mansur Kuma ya bada umurnin a dauki sabbin Malamai 100 domin inganta ilimi
Bayan haka ya bada gudumuwar Naira Miliyan 10 (N10million) a cikin aljihun sa domin aiwatar da wasu kananan ayukkan da kuma aikin Kwamitotin da aka kafa.
SARAKUNA DA DATTAWAN DANDI SUN YABAWA DR. MANSUR
Mai Girma Sarkin Shikon Kamba Alhaji Muhmud Z Fana da dukkan sarakunan da suka halarci wayannan tarukka sun yabawa Dr. Mansur bisa wannan hikima da ya kirkiro, sun bayyana wannan ne karo na farko da wani shugaban Karamar hukuma a Dandi ya nemi ra'ayin mutane kafin aiwatar da ayukka. Sarakunan sunyi alkawalin bashi dukkan gudumuwa da goyon bayan da yake bukata.
Hakama sauran dattawa irin su Col. Muhammad Dole(Rtd), Alhaji Dandare Makera Kyangakwai, Hon Nura Bala Fingilla, Dr. K.K , Alhaji Musa Yamna, Alhaji Sanusi SSS, Alhaji Dandare Boss, Alhaji Umar Kalangun takarda da sauran su da suka halarci taron duk sun yabawa Dr. Mansur Isah.
Bayan wannan za a fitar da cikakken rahoto akan manufofin wannan sabon tsari da Dr. Mansur Isah Kamba ya kirkiro idan za a tace ayukkan da karamar hukuma zata iya, Wanda yafi karfinta Kuma za a turawa Gwamna da ma Shugaban kasa domin aiwatar wa.
Post a Comment
0 Comments