MENENE GASKIYAR MANUFOFIN SHIRIN AGILE?
MENENE GASKIYAR MANUFOFIN SHIRIN AGILE?
SHARHI AKAN RA'AYIN SHEIKH MUHAMMAD BIN USMAN AKAN SHIRIN AGILE BISA CIKAKKEN BAYANI DA GAMSASSUN HUJJOJI
Misali Da JAHAR KEBBI
(Domin fahintar komai akan Shirin AGILE a shiga: www.agileproject.education.gov.ng)
Daga Ahmad Umar
Hankalin mutane da dama dake anfana da shirin AGILE ya fara tashi bisa ra'ayin wani mashahurin Malamin addinin musulunci mai suna Muhammad Bin Usman, a wani faifen bidiyo dake yawo.
Kamar yadda Malamin ya furta cewa " ..Dole mu fada don mun karanta, in ba haka ba munci amanar ilimi" wannan gaskiya ne, haka na nuni da cewa idan ka karanta abu ba ka fada ba kaci amanar ilimi.
Duk wanda ya karanta Shirin AGILE sai ya fadi fahintar sa, su kuma mutane su duba su yanke hukunci da kan su.
Bisa wannan dalilin ne naga ya dace da in rubuta abinda na sani akan shirin AGILE don kada inci amanar ilimi kamar yadda Sheikh ya fada, da fatar sakon zaikai ga Malam da dukkan wayanda keda ra'ayi irin nasa akan shirin AGILE:
1- MENENE MA'ANAR AGILE:
Ma'anar AGILE shine 'Adolescent Girls Initiative for Learning And Empowerment ' Wanda masana suka fassara kamar haka: 'Shirin Tallafawa Ilimin 'Ya'ya Mata Da Inganta Rayuwarsu'.
2- MENENE MANUFAR SHIRIN AGILE?
Babban munufar wannan shiri na AGILE a fahinta ta sune:
i- Ilimatar da 'ya'ya mata (learning)
ii- Koya masu sana'a
(empowerment)
HIKIMA: Hikama shirin AGILE shine kawar da jahilci da talauci a tsakanin Ya'ya mata. Idan macce ta iya rubutu da karatu sannan ta'iya sana'a, zai taimaka mata a gidan miji da sauran rayuwarta na yau da gobe, wannan shine burin AGILE.
3- TSARIN AIWATAR DA SHIRIN AGILE (COMPONENTS):
An raba wannan manufofin AGILE zuwa gida 3, da harshen turanci ana kiran su 'COMPONENTS'. Components 1, Components 2,da Components 3.
Dukkan components din suna da kananan sassa 2 zuwa 3, a karamin sashe na Components 2.1 ne Sheikh ya dogara wajen watsi da dukkan sauran Components din da ma shirin AGILE baki daya. zanyi bayanin:
SHARHI AKAN FAHINTAR SHEIKH MUHAMMAD BIN USMAN AKAN SHIRIN AGILE MUSANMAN COMPONENTS 2.1
1- Sheikh yace Bayahude baya baku kyauta ba tare da shairi a ciki ba, banda ja akan wannan.
Amma Ina son Sheikh ya fahinta kudaden da ake kashewa a shirin AGILE ba kyauta bane, bashi ne daga bankin Duniya zuwa ga jahohin dake bukata kuma babu tilas sai Jaha ta nema a rubuce cewa tanason bashin. Mutane da dama nada rashin fahintar haka. AGILE bashi ne ga jahohi ba Kyauta bane.
-Na biyu Babu tilas akan kowace Jaha, idan Gwamnan Jahar ku yace baida bukatar shirin AGILE shikenan ba za'ayi AGILE a Jahar ba, babu tilas.
- Na ukku, shirin AGILE an tsara shi akan tsawon shekaru 5 ne kawai, ba na dindin bane. Ina fatar Sheikh ya fahinta.
2- Maganar 'Adolescents' Yan mata Yan shekaru 10 zuwa 19: Shi wannan shiri na AGILE musanman a JIHAR KEBBI ba don mata Yan shekaru 10 zuwa 19 kawai aka tanadawar ba kamar yadda Sheikh ya fada, ana gudanar da shi ne ga dukkan makarantun secondary 414 da ke fadin Jihar Kebbi, makarantun Maza da na mata, Yan shekaru 10,19, 20 harma Yan shekaru 40 mata da maza indai suna karatu a makarantar secondary Shirin AGILE ya shafe su. Don haka maganar cewa Yan shekaru 10 zuwa 19 ne kawai ake so fahintar Sheikh ce kawai, ko Kuma ince fassaran kalmar 'Adolescent' ce kawai, Sheikh yayi anfani da ita wajen yanke hukunci akan shirin. Amma a zahiri dukkan daliban secondary mata da maza ne akayi wa tanadin AGILE, kamar yadda yake a Jahar Kebbi.
3- Dalilin fara shirin AGILE da Jahohin Arewa: Sheikh ya sa ayar tambaya akan me yasa aka fara shirin AGILE da jahohin Arewa?
Ansar ita ce; Gwamnonin wayannan jahohin na Arewa su suka rubuta sukace suna bukata, don sun fahinci ALHERIN DAKE CIKIN SHIRIN, Ba Wani ko wata ko wasu da suka zauna suka zabi wayannan jahohi, don haka ba wata Jaha a Arewa ko a Kudu da za'ayi Shirin AGILE ba tare da Gwamnan wannan Jahar ya rubuta ya nuna yana bukata ba. Babu tilas kamar yadda Sheikh ke tuna ni.
4- Game da zargin ba da kudi ga dalibai ; Ba dalibi ko daliba da AGILE ke ba kudi N15,000, kamar yadda Sheikh yace wani ya gaya masa, ba a aiki da jita-jita malam, bincike akeyi, mu dai a Jahar Kebbi iyayen yara ne ake ba kudin, a matsayin fansa ga talla da suke tura yaran. Don haka maimakon su tura ya'yan su zuwa talla sai AGILE ta saye tallan tace su tura ya'ya su zuwa makaranta, wannan shine hikimar kudin. A Jahar Kebbi dai haka nasan anayi, kuma iyaye kalilan ne suka samu wannan damar ba duka ba.
5-Game da alkawalin tura yara kasashen waje yin karatu: Bayan ilimin secondary ba inda AGILE a Jahar Kebbi tayi alkawalin tura wata daliba kasar waje ko wata Jami'a a Nigeria don karatu kamar yadda Sheikh ya fada. AGILE cewa tayi yarinya ta sami ilimi akallan na Secondary, ta iya sana'a sannan taje tayi auren ta. Kada ta zama jahila Kuma ba sana'a. Idan ba a yaba wannan ba, banga dalilin kushe shi ba.
6- Maganar karamin sashe na Components 2.1(Purpose of Components 2.1) da Sheikh ya dogara da shi wajen rusa dukkan sauran kyawawan Components da ma shirin AGILE baki daya.
MENENE COMPONENTS 2.1 YA KUNSA DA YASA SHEIKH YA ZARGI SHIRIN AGILE?
Ga 'screenshot' na wannan Components daga kundin AGILE, don kowa ya karanta yayi hukunci:
FAHINTA TA AKAN COMPONENTS 2.1: A takaice Components 2:1 yayi bayani ne akan yadda za a wayar da kai akan al'adu da tanadi na addini da suke hana baiwa Ya'ya mata ilimi ta hanyar anfani da sarakuna gargajiya, da ganawa ta ido-da-ido domin wayar da kan jama'a cikin lalama.
Ma'ana idan akwai addinin ko al' ada da ya hana ya'ya mata yan'cin neman ilimi sai a wayar masu da kai cikin hikima su bari ya'yan su mata suyi ilimi. Sakon da wannan components 2.1 ke son isarwa kenan.
Addinin musulunci da mafi akasarin al'adun Arewa basu hana Ya'ya mata neman ilimi ba, don haka ba ruwan addinin musulunci da al'adun Arewa da wannan components 2.1.
Kalmar 'Religious' tana nufin addini ko wane iri don akwai jahohin Kiristoti da Yan gargajiya a cikin Shirin AGILE Kamar Jahar Ekiti.
Idan addinin ku da al'adun ku basu hana ya'ya mata neman ilimin ba, ba ruwan ku da components 2.1, bai shafe ku ba.
Idan ma addininku ya hana 'ya'ya mata neman ilimi cewa akayi 'to promote' ba 'to force ko enforce' ba. Ma'ana a wayar da kai, babu tilastawa, Sheikh yafi ni sanin haka.
FAHINTAR SHEIKH AKAN COMPONENTS 2.1.
Ga abinda Sheikh ya fada a matsayin fahintar sa akan Components 2.1 Dana kawo 'screenshot' din sa a sama "Yaran dake Arewa musanman,..mu nuna masu cewa a rabasu da takunkumin addini da al'adu ta yadda uba bai isa yace wa Yar'sa ba, kisa Hijabinki sai tace Baba I am Free.." Subhanallah!
Yanzu don Allah wannan fassaran yayi dai dai da wannan tanadi na components 2.1 da Sheikh ke cewa ya karanta?
A Components 2.1, ba inda aka ambaci Arewa ko takunkumi ko yarinya tayi wa mahaifinta rashin kunya, wannan fahintar Sheikh ce kawai. Don Allah a shiga www.agileproject.education.gov.ng don karin bayani akan dukkan manufofin shirin AGILE.
A dauka ma yadda Sheikh ya fassara wannan tanadin hakane,.. sai ayi gyara,a cire tanadin, amma ba ace dukkan shirin AGILE tsiyane, ya haramta ayi watsi da shi gaba dayan sa.
MISALI: Kamar a Jahar Kano sai a sami rashin fahinta a cikin jami'ar Bayero (BUK) bisa haka sai ace a rusa dukkan Jahar Kano baki daya; Anyi adalci idan akayi haka?. A kan rashin fahintar Components 2.1 ace dukkan shirin AGILE tsiyane a rusa!; babu adalci a wannan danyen hukunci akan AGILE.
MENENE MATSAYIN SHIRIN AGILE A JAHAR KEBBI
A halin da ake ciki shirin AGILE a Jahar Kebbi daidai yake, arziki ne ba tsiya ba kamar yadda Sheikh ya yi zargi. Idan ma akwai tsiya ko shairi a cikin AGILE, mu dai a Jahar Kebbi Alhamdulillah, Allah Ya taimake mu, Alherin shirin kawai muke gani. Don haka kada hankalin duk wani dan Jahar Kebbi ya tashi akan shirin AGILE.... AGILE ALHERI NE IN SHA ALLAHU.
KO AKWAI BOYAYYAR MANUFA A SHIRIN AGILE?
Allah Masani, ni dai ban sani ba, kuma bata bayyana ba, amma duk lokacin da ta bayyana zamu fada, zamu kuma yaketa In sha Allah.
RA'AYIN SHEIKH NA IYASA MA'AIKATAN AGILE CIKIN HADARI
Irin wayannan ra'ayoyi ne suka sa rayuwar ma'aikatan Polio cikin hadari, Inda aka dinga Kai masu hare-hare da zagi da cin mutunci a lokacin da suke aikin su na taimakon jama'a.
AGILE da ma'aikatan ta sai sun tashi tsaye wajen wayar da kan jama'a domin kariyar lafiyar su, domin bakaramar ruwa Sheikh ya debo masu ba akan wannan ra'ayi da ya fada.
SHAWARA ZUWA GA SHUGABANIN AGILE
1- A cikin gaggawa dukkan Jahohi 7 dake aiwatar da shirin AGILE musanman Jahohin Arewa,su gaggauta sake gayyato 'media consultant firm' da sukayi masu aikin wayar da kan ul'umma a baya domin ci gaba daga inda suka tsaya. Kada ayi Kuskuren ba sabbin 'firms' da basu da ilimi akan shirin AGILE . Domin ba karamin wayar da kai (publicity) zai iya share shakkon da zargin da Sheikh bin Usman ya saka a zukatan mutane akan wannan shiri na AGILE.
2-A dinga tantance kalmomin da za ayi anfani da su ; misali maimakon kalmar 'ADOLESCENT' sai ayi anfani da kalmar GIRLS CHILD.
3-A saka Malaman addini a cikin Shirin AGILE a buda masu komai akan shirin, su gyara kurakurai idan akwai.
4- Shugabannin AGILE su kira taron gaggawa na kasa da zai hada dukkan manyan malaman addini da manyan sarakuna da Gwamnonin ayi bayani dalla-dalla, gwari-gwari har kowa ya fahinci alherin AGILE.
SHAWARA ZUWA GA AL'UMMA
1- Don Allah a dinga bincike mai zurfi kafin a yanke hukunci akan kowane irin al'amari
2- Idan an karanta abu ba a fahince shi ba, ko aka fahinci akwai kuskure sai a je wajen shugabannin wannan Shirin a zauna da su a gyara kurakurai, kada a hau mambari ace a rusa shirin baki daya.
3-Kamar yadda Sheikh Muhammad bin Usman ya fada cewa dole mu shiga BOKO mu musuluntar da shi: Shima AGILE din mu shige shi mu musuluntar da shi idan muna shakkon imanin sa, ba mu nemi a halaka shi ba gaba dayan sa. Ba'a zubar da ruwan wanka hade da jariri, sai dai a cire jaririn, sannan a zubar da ruwan.
________________________
Ahmad Umar: (Former Media Consultant KEBBI-AGILE PROJECT)
07038182929
ahmadugamji@gmail.com
Post a Comment
0 Comments