Babu Shairi A Cikin Shirin AGILE

Ƙarin Haske Akan Shirin AGILE Project Daga Bakin Mustapha Shehu PhD State Project Co-ordinator KATSINA...
Naga hudubar Mallam kuma na saurareta sosai, lallai malam ya yi bayanai akan abin da ya fahimta da kuma abin da aka gaya mashi. Yadda na ji malam ya yi magana nasan malam ya karanta ko an bashi bayani akan project ɗin musamman yadda yake faɗin components ɗin wannan shirin. 

Amma gaskiyar magana babu wannan abun a cikin tsarin gudanar da shirin, a iya sani na. Naso a ce Mallam da sauran shuwagabannin mu malamai sun kira wasu daga cikin masu gudanar da shirin ko kuma su samu gwamnati su nemi a kira taron masana domin duba abubuwan da yayi magana a kan su, amma ala kulli halin, ni Ina ganin abin mai sauƙi ne.

Na farko ya kamata masu gudanar da shirin a duk jihohin baki ɗaya su ƙara wajen wayar da kan jama’a da kuma bayyana yadda shirin ya ke domin fahimtar kowa da kowa. 

A jihar Katsina gaskiya duk abin da zamu yi a buɗe yake kuma duk inda aka ga gyara muna amsa domin Al’Qur’ani ne kaɗai daidai Ɗari bisa Ɗari. Lallai abubuwan da malam ya faɗa suna neman a mashi bayani na gaskiya domin tabbas akwai alamun an samo labarin ko bayanin daga hannun wanda ya san shirin ko wani makusanci, amma tabbas an gauraya shi da wasu abubuwan da ba haka suke ba. 

A matsayina na musulmi kuma mai kishin addini na, babu yadda za’a yi a ce ana koyar da irin wannan abun da malam ya faɗa kuma ace mune ke bada goyon baya, Subhanallah. Allah ya sani muna abubuwan mu a buɗe kuma duk abin da a ke gabatarwa to kowa ya san yadda a ke yin sa, sai dai idan akwai wani abu daban wanda muma bamu sani ba, to wannan ana iya zuwa da shi a mamu bayani.

Bani son yin magana mai tsawo akan irin wannan mas’alar amma mai neman bayani ya je makarantun, ko ya nemi malaman ko sauran waɗanda ake gudanar da shirin domin su, zai ji ƙarin bayani.

Daga ƙarshe zan so jama'a su sani shi wannan shirin yanzu haka ana gudanar da shi a wasu ƙasashe kamar su Mauritania, Qatar, Oman, Sudan, Tunisia da sauran su. Yanzu haka wasu daga cikin jihohin kudu na Najeriya suna ƙorafin cewa ba’a saka su cikin shirin ba.

Ni a gani na kuma har yanzu ina kan wannan ra’ayin, gaba ɗaya shirin ma, da ace tun can baya shuwagabanni da sauran ma’aikata sun yi wa harkar ilimi adalci an cire son rai, da bamu ma buƙatar wani tallafi ko bashi don gyaran ƙasar mu. Kuɗin da muke kashewa wajen harkar ilimi sun linka waɗanda ake ba ƙasar mu bashi ko tallafi nesa ba kusa ba.

Amma kuma dole idan akwai abin da ake ganin ya Saɓama shari’a dole ayi magana, yin magana don gyara komin ƙanƙantar gyaran yafi yin shiru tabbas, illa iyaka a Ɗan ƙara bincike wajen masu ruwa da tsaki kamin yanke hukunci su kuma masu gudanarwa su ƙara ƙoƙari wajen sanyo kowa da kowa wajen gudanar da shirin domin ƙara samun fahimta.

Ni a gani na gaba ɗaya shirin da ire-iren su, bamu ma buƙatar su a Najeriya saboda kuɗaɗen da ake kashewa wajen gudanar da shirin ko kusa basu kai waɗanda ake kasafin kuɗin shekara shekara (budget) dasu ba a jihohin mu. Illa iyaka yadda ake kashe kuɗaɗen talakkawa ba tsari da tausayi, shi ya kaimu ga haka.

 Amma iyakar fahimta ta wallahi bamu Buƙatar tallafin kowa, kawai a yi shugabanci da amana a kashe kuɗaden talakkawa da gaskiya. Idan za’a koma wa gaskiya da amana (wannan kuma dukkan mu ya Shafa babu wani wane) to yau ana iya rufe irin waɗannan programmes ɗin gaba ɗaya, to amma son rai da son abin duniya baya bari. 

Wallahul Musta’aan.

Post a Comment

0 Comments