Bin Uthman Ya Amince Da Zama Da Shugabannin AGILE
SHIRIN AGILE
SHAYKH MUHAMMAD BIN UTHMAN YA AMINCE DA A ZAUNA DA SHI DOMIN GANO BAKIN ZARE
"A shirye nake mu zauna domin gano bakin zare da duk wanda ke da bukatar haka."____ Inji Sheykh Bin Uthman a martanin sa ga rubuce rubucen da suka biyo bayan ra'ayin sa akan shirin AGILE
Sakamakon martani da suka biyo bayan furta ra'ayin sa akan shirin AGILE, fitattacen Malamin addinin musulunci Sheykh Muhammad bin Uthman ya fitar da wata doguwar budaddan wasika inda yayi bayani dalla-dalla akan dalilin sa na zargin Shirin AGILE.
Sheykh Bin Uthman ya ambaci wasu kalmomi da akayi anfani da su a Components 2.1 a matsayin madogaran sa na zargin Shirin AGILE.
An mayar wa Sheykh Bin Uthman martani daga Jahohi 3 daga cikin jahohi 7 ne da ake aiwatar da shirin AGILE.
A Jahar Kano, gamayyan kungiyoyi 11 suka hadu sukayi binciki suka ce Shirin AGILE bai da matsala.
A Jahar Kebbi Kuma tsohon jami'in tuntuba a fannin yada labarai na Shirin AGILE a Jahar Kebbi, Ahmad Umar ne yayi sharhi a madadin Shirin AGILE na Jahar Kebbi
A Jahar Katsina Kuma, shugaban Shirin AGILE na Jahar ne da Kansa Dr. Mustapha Shehu, yayi Karin haske akan ra'ayin Sheykh Bin Uthman.
A cikin hikima, Sheykh Bin Uthman ya zabi martanin Jahar Katsina, wajen rubuta budaddiyar wasikar, kasancewar Shugaban Shirin ne da Kansa yayi martanin.
Ga cikakkar wasikar a kasan wannan layin, asha karatu lafiya:
________________________
AKAN BATUN SHIRIN AGILE DAI
Salaamun alaikum.
Na yi farin ciki kan ƙarin hasken da Dr Mustapha Shehu(State project co-ordinator KT) yayi kan Khutbata wadda na gabatar a Maiduguri ranar Jumu'ah 24=11=2023
Ga nawa ƙarin hasken:
1- Babu wanda ya gaya min wani abu kan AGILE.
Tattaunawa ce tsakaninmu ta kai ni ga yin bincike kuma na bayyana abinda bincike ya gwada min. Kuma a takaice matuka na faɗa.
2- Maganar "Components" ai ba sai wani ya gaya min ba tunda rubutawa masu shirin suka yi kuma na karanta na kuma fahimci abinda suke nufi.
3- Ɗan uwa maigirma yana cewa:
"Amma gaskiyar magana babu wannan abun a cikin tsarin gudanar da shirin, a iya sani na"
Tambaya:
a/ Wani abu ne "WANNAN ABUN" da babu shi cikin maganata kan shirin? Ya kamata ya bayyana shi. Ko da yake ya ce a iya saninshi. Ma'abota ilimi suna cewa:
"إن عدم العلم بالشيء لا يعني العلم بعدمه"
Wato:
"Rashin sanin samuwar wani abu ba ya kore samuwarshi"
b/ A cikin Sub-component (na AGILE),
2 .1: ga abinda a ka ce:
"Promoting social and behavioural CHANGE(manyan baƙaƙen nawa ne) through communications....."
Tambaya:
👉 Wani irin canji a ke so a kawo mana a nan?
👉 Wani tsari ne a ke so a canza? Idan tsarin kuma ya dace da addinin musulunci fa?
Na san ku ba za ku yarda ba tunda kuna kishin Musulunci, to amma haka yake a kundin tsarin AGILE. To sai mu yi shiru?
Kundin kuma yaci gaba da cewa a ƙarƙashin dai Sub-component 2.1:
"The objective of this component is to promote a SHIFT(upper cases mine) in social and cultural norms and perceptions which act as barriers to girls' schooling...."
Tambaya:
👉Mecece ma'anar SHIFT(mine)a nan?. A yi "shifting" daga ina zuwa ina? Bai kamata mu sa ido sosai ba dan kada "ayi mana shigo-shigo ba zurfi ba"?
Har wa yau a dai cikin shi wannan ɓangare na kundin ga abinda suka rubuta:
"This sub-component seeks to address the cultural, social and RELIGIOUS NORMS (mine)that impeded girls' access to education...."
Tambaya:
👉Wane addinin ne a jihohin gwaji ko aiwatarwa (implementing states) na Arewa musamman Arewa maso yamma da kuma maso gabas ke da RELIGIOUS NORMS( dokoki na addini) waɗanda ke yi wa karatun 'ya mace tarnaƙi?
👉Kuma wani irin tarnaƙi(impeding) ne?
👉In ba Musulunci ake nufi ba, me ya sa babu jiha ɗaya cikin jihohin South East ko na South South cikin jerin jihohin gwaji (implementing states?)
Daɗin daɗawa, ga wata ƙarfafawa da dai kundin ya sake jaddadawa a s/c 2.1 cewa:
"The purpose of sub-component 2.1 is to promote a shift in socio-cultural norms and RELIGIOUS BELIEFS(mine) that act as barriers to girl- child education. It hopes to CHANGE THE NARRATIVE through various communication campaign....."
Tambaya:
👉Kamar dai tambayar baya ne, ba sai na maimaita ba.
Dangane da tsokacin da ɗan uwa maigirma yayi cewa ya kamata malamai da shugabanni su kira masu gudanar da shi wannan shiri domin tattaunawa, wannan shawara ce mai kyau amma a lokacin da masu gabatar da shirin suka ɗauko shirin domin aiwatarwa, sun taɓa tsayawa sai sun gama tuntuɓar malamai tsaf tukun suji hukuncin Allah kan kowace kalma da lafazi da kuma ƙuduri rubutacce ko magananne kafin su fara aiwatar wa?
Me yasa ba sa ƙimanta Musuluncin ta hanyar dakatar da kome sai sun ji fatawar Malamai tukun? Nan an ƙimanta addinin musulunci? Jihohin gwajiin nan duk Nigeria akwai inda ya kai su yawan musulmi ne. Kano, Kaduna, Katsina, Kebbi, Borno. Ko ba su ba ne? Akwai Musulmi ne a Plateau da Ekiti kamar waɗannan na saman da na ambata?
Duka wanda zai fara yin wani abu da ya shafi al'ummah ba sai ya bi dokokin ƙasa tukun ba?
Me yasa shi Musulunci ba a yi masa irin wannan girmamawar? Sai a fara aiwatar da abinda ake bukata gaba gaɗi sai in masana cikin Malamai sun ga wani abu ba daidai ba in sun yi magana sai kuma ka fara jin gunaguni. Dan haka ni a fahimtata, su masu ɗauko ire-iren waɗannan shiry- shirye su kawo cikinmu ai muna musu kyakkyawan zato cewa ci gaban al'ummah suke nufi, to amma KADA A CIRE WANDO TA KA, TA ƘAFA ZA'A CIRE!
Ko shakka babu, in an yi shirin ta hanyar mutunta addininmu, Malamanmu da al'adunmu kyawawa, zai taimaka matuƙa gaya.
Waɗanda suka zuba/kuma suke zuba kuɗaɗensu domin wai "ci gabanmu", anya:
YAUSHE KURA TA ZAMA TA GARI DA HAR ZA'A BATA TALLAR NAMA, KUMA KAYI TSAMMANIN WANYEWA DA ITA LAFIYA?!!
Daga ƙarshe ni kam da dukkanin al'ummar Musulmi wallahi muna kan gaba wajen ilmantar 'ya'ya musamman mata amma ba bisa fahimtar wasu ba waɗanda gabarsu da addininmu da suke yi a fili take. Karanta ayah ta 217 cikin Baƙarah da kuma ayah ta 89 cikin suratun Nisa da makamantarsu.
A yi haƙuri na ɗan tsawaita amma gaskiya ban faɗi ma ɗaya ba cikin uku 1/3 na abinda zan faɗa kan irin wannan mas'ala.
A shirye nake mu zauna domin gano bakin zare da duk wanda ke da bukatar haka.
ALLAH KA NUNA MANA GASKIYA KA KUMA BAMU IKON BINTA, KA KUMA NUNA MANA ƘARYA KA KUMA BAMU IKON KAUCE WA DA KUMA GUJE MATA, aamin.
- Abuu 'Aasim ( Shaykh Muhammad Bin Uthman )
Post a Comment
0 Comments