Dan'majen Gwandu Ya Gaji Kyauta ne daga mahaifin sa
Dan'majen Gwandu Ya Gaji Kyauta ne daga mahaifin sa.
GADON KYAUTA: Duk Kyautan Dan'majen Gwandu bai Kai mahaifin sa ba__inji abokin karatun sa, Abubakar Chamucha
Sakamakon bincike da nazari akan zuciyar kyauta da Allah Ya horewa Shugaban Hukumar kula da Sararin Samaniya ta Nijeriya, Injiniya Ahmed Umar Farouk (Dan'majen Gwandu/ Gamjin Kabi) ya nuna cewa ya gaji wannan aikin alherin ne daga mahaifin sa Marigayi Yarin Suru, Malam Umaru Raha, Jikan Sarkin Gwandu na 10 Umaru Bakatara Bn Ibrahim Khalilu.
Kamar yadda daya daga cikin Mawakan Dan'majen Gwandu, Musa Na'Allah yake fada a daya daga cikin wakokin da yayiwa inda yake cewa '..kyauta in za a baka sai an Darje'__ Ashe duk darjewar da Dan'majen Gwandu keyi idan zai bada kyauta, bai kai mahaifin sa ba, Inji Abubakar Maliki Usman (Chamucha).
Abubakar Chamucha yace Kyautar Dan'majen Gwandu ta gado ce Kuma tun suna makarantar firamari har zuwa Sakandare da Polytechnic kayan Dan'majen Gwandu kayan jama'a ne.
" Babu bakin ciki a rayuwar Dan'majen Gwandu, mutun ne mai alheri fiye da yadda ake gani, wannan gida da muke wannan hira da Kai Dan'majen Gwandu ne ya gina mini shi kyauta" Inji Abubakar Chamucha
Abubakar Chamucha ya buga misalai da dama dake tabbatar da kyautan Dan'majen Gwandu.
Chamucha yace ba so Daya ba ba sau Biyu ba yasha ganin wayanda Dan'majen Gwandu zai yiwa kyauta maimakon suyi dariya sai kawai su fadi kasa suna kuka saboda rudewa da yawan kyautar.
Amma yace duk da haka Dan'majen Gwandu bai kai mahaifin sa yin kyauta ba.
Yace anyi lokacin da zaran anyi albashi abokan mahaifin Dan'majen Gwandu zasu tabbatar da ya sayi kayan abinci da sauran bukatun iyali, in ba haka ba kafin gari ya waye duk ya rabewa jama'a albashin.
Ance mahaifin Dan'majen Gwandu Marigayi Yarin Suru har bashi yakeci don yayiwa jama'a hidima, domin ba a tambayar sa yace babu, sai dai yace a Jira, sai yaje yaci bashi yazo ya biya wannan bukatar.
KO DAN'MAJEN GWANDU ZAI IYA GADON SABON BABAN SA, DR. NASIR IDRIS (KAURAN GWANDU) WAJEN KYAUTA
Har yanzu Dan'majen Gwandu nada kalubale, domin Allah Ya sake hada shi da sabon uba da keda wuyar gado wajen kyauta.
Yawan Alherin da Allah Ya azurta Dr. Nasir Idris Kauran Gwandu yasa yan'adawa ke sukan sa,.. saboda Allah ya rufe masu hankali har suke ganin yin kyauta laifi ne.
Dan'majen Gwandu ya gaji Kyauta dama da hauni, kuma ya nuna ya gaji kyauta ta hanyar ci gaba da yiwa mutane hidima.
"Allah Ya bi Dan'majen Gwandu da halinsa, saura sati 3 kacal yayi ritaya, Allah Ya bashi wannan kujeran ta MD, NAMA" Inji Abubakar Chamucha

Post a Comment
0 Comments