WA KEYI WA KAURAN GWANDU ZAGON KASA?

Waye Keyi Wa Kauran Gwandu Zagon Kasa?


RASHIN TAIMAKAWA MATASA MASU SON SHIGA AIKIN TSARO: Kasawar Gwamnatin Jihar Kebbi Ne Ko Zagon Kasa Ne?

 -An Dakatar Da Taimakawa matasan Kebbi masu shiga aikin Soja

-Anyi bikin yaye jami'an Yan'sanda a Sokoto, jihar Kebbi ce kawai ta kasa tura wakilinta kamar yadda aka saba

-Jihar Kebbi ce kawai ta kasa tura wakilinta a jarabawan shiga makarantar Yan sanda a jihar Kano

-Jihar Kebbi ta kasa bayar da kudin sa Ido wajen daukar aikin 'Custom'

-Shawara ga Mai girma Gwamnan Jihar Kebbi

Ga dukkan alamu akwai masu yiwa mai girma Gwamnan Jihar Kebbi Dr Nasir Idris (Kauran Gwandu) zagon kasa ta hanyar hanashi ko kuma karkatar da taimakon da Gwamnatin jihar Kebbi ta saba bayarwa ga matasa masu son shiga aikin Soja da Yan'sanda da sauran su.

Tsawon shekaru 8 na Gwamnatin Atiku Bagudu da ta gabata, ba a taba samun matsala ba wajen taimakawa wayanan matasan.

 Amma abin mamaki tun zowan wannan Gwamnatin ta Dr. Nasir Idris (Kauran Gwandu) da aka shaida da kyauta da alheri komai ya lalace, dukkan taimakon da Gwamnati ta saba bayarwa duk an datakatar da su. Idan kuma yana bayarwa to KEBBI-TRUST na tabbatar mishi cewa akwai masu yi masa zagon kasa dake karkatar da wannan taimakon zuwa cikin aljifan su.

- An Dakatar Da Taimakawa matasan Kebbi masu shiga aikin Soja
Tsawon shekaru 8 na Gwamnatin Atiku Bagudu duk lokacin da za a dauki aikin Soja yakan ware kudi Tsakanin Naira miliyan 10 zuwa miliyan 15 domin ba wayanan matasan tallafi da kuma sauran ma'aikatan sojaji da na Career ofis domin komai yaje dai dai.
Amma tun zowan wannan Gwamnatin ta Dr Nasir Idris kudin mota zuwa Zariya kawai ake samarwa, ko 'Pure water' ba a taimakawa wayanan matasan da shi.
Idan kuma Gwamna na bayar da taimako ga wayanan matasan to taimakon Bai kawo gare su, akwai Yan zalamar dake awon gaba da wannan tallafin.


- Anyi bikin yaye jami'an Yan'sanda a Sokoto, jihar Kebbi ce kawai ta kasa tura wakilinta kamar yadda aka saba

A ranar 7/10/2025 an yaye sabbin jami'an Yan'sanda a makarantar huron Yan sanda dake Farfaru a Jahar Sokoto, ko wace jiha ta tura wakilinta da taimakon daga Gwamnonin su, Amma jihar Kebbi ta kasa tura kowa ballantana taimako daga Gwamna.
Wannan yasa yaran jihar Kebbi zama marayu a Nijeriya da Kuma zubar da hawaye saboda saka su cikin kwandon mantuwa da Gwamnatin jihar Kebbi ta yi.



- Jihar Kebbi ce kawai ta kasa tura wakilinta a jarabawan shiga makarantar Yan sanda a jihar Kano

Har ila yau a ranar 11/10/2025 ko wace jiha a Nijeriya ta tura wakilinta domin tabbatar da matasan jihar su sun Sami shiga makarantar Yan'sanda dake Wudil a jihar Kano, Nan ma jihar Kebbi ta kasa fitar da kudi ta tura wakilinta, ance guraben da aka kebewa Jihar Kebbi an wawushe su amba wasu jahohi saboda rashin wakilan jihar Kebbi a wajen 'admission screening interview '.
Nan ma anga matasan Jahar Kebbi na ta rusa kuka saboda rashin kulawa daga Gwamnatin jihar Kebbi.


 -Jihar Kebbi ta kasa bayar da kudin sa Ido wajen daukar aikin 'Custom'
 Duk lokacin da za a dauki ma'aikata aiki a hukumar 'Custom' da Immigration da sauran su, Gwamnatin Kebbi ta kan ware makudan kudade ta hannun Career office domin taimakawa matasan jihar Kebbi, ance shima wannan taimakon na musanman an dakatar da shi a halin da ake ciki.

'Career office' dake da alhakin gudanar da dukkan wayanan tsare tsare, Shima bai tsira ba, ance an rufe shi, Wanda ke nuna matukar lalacewar al'ammura akan taimakawa matasan jihar Kebbi dake neman aikin tsaro da kuma a matakin Gwamnatin Tarayya.

 -Shawara ga Mai girma Gwamnan Jihar Kebbi

Mai girma Gwamna, wayanan matasan sun sadakar da rayuwar su da dukkan wani buri najin Dadi, ta hanya jingine maganar zuwa 'University ' ko 'Polytechnic' ko takaran kujeran siyasa, don kawai su shiga aikin tsaro su kare mutuncin mu daga yan'taadda, ko su kashe ko a kashe su, don haka ba wayanda suka dace da ayi wa alheri ko kyauta kamar su.

A takaice Mai girma Gwamnan ga shawarwari guda ukku (3):
1-   A gudanar da bincike a gano wanene baiyi aikin sa ba, har sunan Gwamna da Gwamnatin jihar Kebbi ke neman baci a idanun duniya akan rashin taimakawa wayanan matasan jihar Kebbi 

2-  Idan ba abada wannan taimakon, 'Your Excellency' ayi hakuri a ci gaba da bayar da wannan taimakon kamar yadda Gwamnonin baya sukayi.

Idan kuma ana bayarwa, sace kudin akeyi, ayi bincike a gano barayin dake sace kudin a hukunta su, domin ya zama darasi; Kuma a wanken sunan Gwamna da Gwamnatin jihar Kebbi bisa wannan badakalar

3-  Ayi hakuri a sake bude 'Career office' da akace an rufe, a basu cikakken yan'ci da wadatattun kudade domin taimakawa matasan jihar Kebbi da ke neman aikin tsaro da sauran su.

Post a Comment

0 Comments