TKG Ta Zama Jami'ar Siyasar Jihar Kebbi




TKG CE JAMI'AR SIYASAR JAHAR KEBBI: Babban Farfesa Siyasar Jihar Kebbi Sanata Adamu Aleiro ya bada goyon bayan sa ga tafiyar TKG

Abu kamar wasa Karamar magana ta zama babba; Bayan gwagwarmaya da jajircewa da Kuma yakar masu zagon kasa da kananan maganganu yanzu dai ta tabbata kungiyar goyon bayan zarcewar shugaba Tinubu da Mai girma Gwamnan jihar Kebbi Dr. Nasir Idris (Kauran Gwandu) watau 'Tinubu Kauran Gwandu Continuity Movement Group (TKG) yanzu ta zama tamkar Jami'ar siyasa a Jahar Kebbi, in da a kullum sai ta dauki sabbin dalibai, Kuma kullum sai ta yaye wasu daliban.

Tuni dai babban shehi Malami watau Farfesa na Siyasar Jihar Kebbi H.E. Sen. Muhammad Adamu Aleiro ya kawo ziyara a wannan Jami'ar ta Siyasar Jihar Kebbi (TKG) inda ya aminci da wanzuwar ta tare da Sanya mata Albarka.
DALILIN KIRKIRO KUNGIYAR TKG

Idan za a tuna, bayan kammala zaben 2023, jam'iyar PDP ce ta lashe dukkan kujerun Sanatoti 3 da ake da su a jihar Kebbi, ta Kuma cinye kujeru 4 daga cikin 8 na Yan majalisan wakilai.

Itama kujeran Gwamna da 'Inconclusive' aka yi kama kama aka kawo ta.

Wannan na nuna rauni a tafiyar APC a Jahar Kebbi, don haka lokacin da wasu suka sa gaba wajen neman kwangiloli da mukamai don samun na cefane, shi Kuma Injiniya Ahmed Umar Farouk (Dan'majen Gwandu Gamjin Kabi) abinda yasa gaba shine yadda za a dinki waccan rauni da ya hanga a zaben 2023 don karawa APC azama, karfi da Kuma karbuwa ga jama'a.

Saboda haka sai Dan'majen Gwandu ya kirkiro da TKG domin taimakawa a rufe wancan rauni da APC ta fuskanta a zaben 2023

ABIN MAMAKI.....

Abin mamaki shine yadda wasu daga cikin wayanda suka kira kansu abokan Gwamna suka kasa fahintar hikima da kokarin da Dan'majen Gwandu keyi na kare mutuncin Gwamna da jam'iyar APC ta hanyar kirkiro da TKG..sai kawai suka ba Gwamna mummunar shawara cewa a Dakatar da tafiyar TKG a rufe ofishinta a je gida ata bacci, ba ruwan su da wancan raunin da Dan'majen Gwandu ya hango yake kokarin rufewa...Anya abokan gaskiya zasuyi wa Gwamna wannan zagon kasa?


GASKIYA TA YI HALINTA...
Hausawa na cewa HASSADA GA MAI RABO TAKI; bayan dakatar da TKG na kusan shekara daya, Gwamna na nazarin halayan wayanda suka bada shawaran rufe TKG, Yaga ko zasu kirkiro da nasu kungiyar domin taimaka masa da kuma jam'iyar APC, Amma shiru,. bayan tarawa kawunan su kudi da kuma tunanin yadda za a basu takara a 2027 ba abinda suka sa gaba, wannan yasa His Excellency ya ankara yace TKG ta dawo ta ci gaba da ayyukkan Alherin ta, na taimakawa Jam'iyar APC da magoya bayan Mai girma 
Gwamna, Dr. Nasir Idris (Kauran Gwandu)


TKG TA KAFA TARIHI...

Tun kirkiro Jahar Kebbi ba a taba samun kungiyar da Shugaban Jam'iya na kasa tare da Shugaban Jam'iya na jiha da mukaraban su, da kansu suka zo suka bude ta ba sai TKG.. 

Shugaban Jam'iya na kasa ba zai bude kungiya ba sai SHUGABAN KASA YA Sani, don haka TKG TA SHIGA VILLA...BABA TINUBU YA SANYA MATA ALBARKA 



TKG TA ZAMA TAMKAR JAMI'A (UNIVERSITY) NA SIYASAR JAHAR KEBBI 

La'akari da manyan mutane irin Gwamnan jihar Kebbi Dr Nasir Idris (Kauran Gwandu), Sanata Adamu Aleiro, Abba Aliero, Sulaiman Jarman Kabi, Umar Dutsin Mari da sauran su da kuma manyan kungiyoyi irin su Kungiyar Matar Shugaban Kasa (Remi Tinubu Support Organization) Kungiyoyin mata da matasa, kungiyoyin kwararrun Yan kasuwa da masana dabam dabam da sauran su, dake kaikawo a ofishin TKG a kullum tare da nuna goyon bayan su, sun tabbatar da TKG ta zarta kungiyar siyasa sai dai kawai a kirata Jami'ar siyasa ta jihar Kebbi.




DAN'MAJEN GWANDU Ya Zama Farfesan (Professor) A Siyasar Jihar Kebbi 
Yaki sai da Kwamanda,.. haka ma Jami'a sai da Farfesa__Don haka la'akari da gumurzu da turnuku da Dan'majen Gwandu ya yi har ya samu wannan Nasara Kuma a matsayin sa na wanda ya kirkiro da TKG (Jami'ar Siyasar Jihar Kebbi) da Kuma daukar nauyinta ba shakko ya cancan ci a kira shi FARFESA (Professor) A SIYASAR JAHAR KEBBI.
_______________________
Ahmed Umar 
Mawallafin Jaridar Kebbi-Trust 
ahmadugamji@gmail.com 
07038182929

Post a Comment

0 Comments