Tattaunawa Ta Musanman Da Hon. Kabiru Ibrahim Masama (Kashi Na 3)
Tattaunawa Ta Musanman Da Hon Kabiru Masama (Kashi Na 3)
A ci gaba da tattaunawa ta Musanman da Jaridar Kebbi-Trust Online keyi da Alhaji Kabiru Ibrahim Riskuwa Masama, Dan Takaran kujeran Dan majalisan Jihar Kebbi Mai Wakiltar Karamar Hukumar Gwandu a karkashin Tutar Jam'iyar ADC,..Hon Kabiru ya bayyana cewa takaran sa ba gudu ba Jada baya
_________________________
Kebbi-Trust: An ga ka ziyarci tsohon Ministan Shari'a Abubakar Malami SAN, mene ne alakar ka da shi?
Hon. Kabiru Masama: Dr. Abubakar Malami SAN, CON shine madugun sabuwar tafiya a Jahar Kebbi, kuma yana cikin manyan shugabanin Sabuwar tafiya a matakin kasa, don haka ubane Kuma shugaba a gareni.
Don haka na ziyarce shi ne Domin nuna goyon baya na ga tafiyar sa da Kuma jam'iyar ADC, da Kuma sanar da shi niyyata ta tsayawa takaran Dan majalisan Jihar daga karamar Hukumar Gwandu
Kebbi-Trust: Ko kana da niyar jayewa wani wannan takarrar?
Hon. Kabiru Masama: Ko kusa, a kara kawai, mai rabo ya dauka.
Kebbi-Trust: Idan Mun fahinceka, takaranka ba gudu ba ja da baya kenan ko?
Hon. Masama : In Sha Allah
Kebbi-Trust : Kauran Gwandu shago ne na siyasa, duk ya buga sai an kama kasa, anya zaku iya daukar bugun kaura
Hon. Masama : Tunda kun kwatanta Kauran Gwandu da shago, mu Kuma Gwaninmu, Dr. Abubakar Malami SAN zamu iya kwatanta shi da AUDU KAI KADAI GAYYA, Ka tambayi wayanda suka San tarihi.. ko Shago ya taba kashe Audu Kai kadai Gayya (Dariya...)
Kebbi-Trust : Toh Allah Ya bada nasara
Hon. Kabiru Masama: Amin Ya Hayyu Ya Qayyum..

Post a Comment
0 Comments