Tattaunawa Ta Musanman Da Hon Kabiru Masama (Kashi Na 2)

SAMAR WA MATASA AIKI DA TAIMAKAWA MANOMA DA YAN KASUWA SUNE MANUFOFI NA

A ci gaba da tattaunawa ta Musanman da Jaridar Kebbi-Trust Online keyi da Alhaji Kabiru Ibrahim Riskuwa Masama, Dan Takaran kujeran Dan majalisan Jihar Kebbi Mai Wakiltar Karamar Hukumar Gwandu a karkashin Tutar Jam'iyar ADC,..Hon Kabiru ya bayyana manufofin sa da Kuma wasu muhimman batutuwa
_________________________


 Kebbi-Trust: Akasarin wayanda ke kan kujeran siyasa a Gwandu kamar iyaye ne a gareka me yasa zaka nemi yin takara da su?

 Hon. Kabiru Masama: Kundin tsarin mulkin Najeriya ne ya bani damar yin takaran dukkan kujeran da nike bukata. 

Na biyu a al'ada ta Hausa-Fulani, idan uba na kan aiki, sai karfin Dan sa ya kawo, to wajibi ne Dan ya taimaka ya amshi aikin don ya hutar da uban nasa.

A matsayina na Da Mai ladabi da biyayya, na fito ne don in ba Baba dama yaje gida ya huta, ya barmu da wannan aikin Mai matukar wahala

Lokaci yayi da ya kamata wayanan iyayen namu su hakura, su ba matasa dama, Sannan su biyo mu da shawarwari

 Kebbi-Trust: Idan Allah Ya baka wannan kujera, me zakayi wa jama'a karamar Hukumar Gwandu?

 Hon. Kabiru Masama: Idan Allah Ya ba ni wannan kujeran, In Sha Allah zan samar da ayukka ga matasa, zan sa a koyawa jama'a sana'a da kuma basu wadattaccen jari.

Zan Kuma yi tsayin daka inga an samar wa karamar Hukumar Gwandu Ayukkan ci gaban jama'a kamar tituna, makarantu, asibitoti, wutan lantarki, ruwan Sha da sauran su.

Haka manoma da Yan kasuwa zan tabbatar da an basu abinda zai inganta sana'o'in su.

 Kebbi-Trust: An ga ka ziyarci tsohon Ministan Shari'a Abubakar Malami SAN, mene ne alakar ka da shi?
 Hon. Kabiru Masama: Dr. Abubakar Malami SAN, CON shine madugun sabuwar tafiya a Jahar Kebbi, kuma yana cikin manyan shugabanin Sabuwar tafiya a matakin kasa, don haka ubane Kuma shugaba a gareni.
Don haka na ziyarce shi ne Domin nuna goyon baya na ga tafiyar sa da Kuma jam'iyar ADC, da Kuma sanar da shi niyyata ta tsayawa takaran Dan majalisan Jihar daga karamar Hukumar Gwandu.
_________________________

Mu hadu a Kashi na 3....
________________________

Post a Comment

0 Comments