Ikon Allah A Tarihin Sabon Shugaban Sojojin Ruwa

Rear Admiral Idi Abbas: Ɗan Jos da Aka Hana Shaidar Zama Ɗan Ƙasa, Amma Ya Zama Shugaban Sojojin Ruwan Najeriya 
Sabon Shugaban Sojojin Ruwa na Najeriya (Chief of Naval Staff), Rear Admiral Idi Abbas, asalin ɗan jihar Plateau ne, daga birnin Jos, amma tarihin rayuwarsa ya ɗauki salo mai ban mamaki.

Rear Admiral Idi Abbas, wanda aka haifa kuma ya tashi a Jos, ya nuna sha’awarsa ga aikin soja tun yana matashi. Sai dai a lokacin da yake neman shiga sojan ruwa, wasu matsaloli na siyasa da ƙabilanci suka sa aka hana shi samun shaidar zama ɗan asalin jihar Plateau, wadda ake buƙata kafin neman aikin gwamnati a lokacin.

A lokacin da Idi Abbas ya ga ba zai samu shaidar zama na Filato ba, sai ya garzaya Kano, ƙaramar hukumar Nasarawa inda mahaifin shi ya fito inda nan take ya samu shaidar kuma ya samu aikin sojan ruwa. 

Daga nan ne rayuwarsa ta ɗauki sabon salo. Ya shiga makarantar horar da sojojin ruwa na Najeriya, inda ya kammala sakamako mai kyau. 

 A yau, wannan haziƙin daga Jos ya zama babban kwamandan rundunar sojojin ruwa ta Najeriya, abin alfahari ga Najeriya baki ɗaya, musamman jama’ar Arewa. 

Wasu masu sharhi sun bayyana cewa labarin Rear Admiral Idi Abbas yana zama darasi ga matasa, cewa rashin samun goyon baya daga gida baya nufin rashin nasara.


Allah kasa ya yiwa Kano da Kanawa Halicci Kamar yadda suka rungume shi a Lokacin da wasu suka nuna Masa kabilanci da Kiyayya!

Idan za a tuna Marigayi tsohon shugaban kasa Janar Murtala Ramat Muhammad da Janar Sani Abacha asalin su daga Jahar Borno suke amma Kano ta basu masauki har suka zama abinda suka zama.

Tsohon Gwamnan Kano Ibrahim Shekaru shi Kuma daga Jihar Yobe ya fito__ wannan ya zama darasi ga masu kyama da Kuma masu kaunar baki

Post a Comment

0 Comments