Alakar TKG Da TKT

Alakar TKG Da TKT

Dalilin Da Yasa Dan'majen Gwandu Ya kirkiro da TKG Ya Kuma Taimakawa TKT Da Naira Miliyan 100 (N100million)

Mutane da dama na tambayar alaka ko akasin haka tsakanin kungiyar TKG da Dan'majen Gwandu ya kirkiro da Kuma kungiyar TKT da aka kirkiro daga baya. Don haka zamuyi dan takaitaccen sharhi akan wayanan manyan kungiyoyi biyu.

ALAKAR TKG DA TKT

Babban alakar TKG Da TKT shine tallata Ayukkan shugaban kasa Alhaji Bola Ahmed Tinubu da kuma Gwamna jihar Kebbi Dr. Nasir Idris (Kauran Gwandu) domin a sake zaben su karo na biyu a 2027 In Sha Allah.

Don haka TKG da TKT yan'tagwaye ne daga uwa daya uba daya watau- 'jam'iyar APC'.


DALILIN KIRKIRO KUNGIYAR TKG

Idan za a tuna, bayan kammala zaben 2023, jam'iyar PDP ce ta lashe dukkan kujerun Sanatoti 3 da ake da su a jihar Kebbi, ta Kuma cinye kujeru 4 daga cikin 8 na Yan majalisan wakilai.

Wannan na nuna rauni a tafiyar APC a Jahar Kebbi a 2023, don haka lokacin da wasu suka sa gaba wajen Neman kwangiloli da mukami don samun na cefane, shi Kuma Injiniya Ahmed Umar Farouk (Dan'majen Gwandu Gamjin Kabi) abinda yasa gaba shine yadda za a dinki waccan rauni da ya hanga a zaben 2023 don karawa APC azama, karfi da Kuma karbuwa ga jama'a.

Saboda haka sai Dan'majen Gwandu ya kirkiro da TKG domin taimakawa a rufe wancan rauni da APC ta fuskanta a zaben 2023, da kuma yiwa Shugaba Tinubu da Gwamnan Jihar Kebbi Dr Nasir Idris (Kauran Gwandu) da dukkan yan takaran jam'iyar APC aiki domin samun nasara a zaben 2027 In Sha Allah.


DALILIN KIRKIRO KUNGIYAR TKT
Akwai sabanin fahinta akan dalilin kirkiro da kungiyar TKT watau 'Tinubu-Kaura Two Times'- a fahintar wasu mutane an kirkiro ta ne domin hada magoya bayan TKG da Yan Haramtacciyar kungiyar 9-11 da kuma sabbin Yan PDP irin su Senator Adamu Aleiro da sauran su da suka dawo APC domin ayi tafiya daya a APC

Sannan kuma akwai mutanen da suka fassara kirkiro da TKT a matsayin kishiya ga TKG ..Wasu Kuma sukace an kirkiro da TKT ne domin a ragewa yayarta TKG karfi ko Kuma a tilasta TKG ta narke ta hade da TKT...Allah Masani


 HAR YAU DAN'MAJEN GWANDU NE UBAN TKT WAJEN BAYAR DA KAYAN AIKI__INDA YA TAIMAKA MASU DA NAIRA MILIYAN 100 (N100M) DOMIN SU TSAYA DA KAFAFUWAN SU
Koma manene dalilin kirkiro da TKT,.. a wajen Dan'majen Gwandu ko gizau;.. asalima shi ya na ganin TKT a matsayin kungiyar da zata rage mishi aikin da yasa gaba a TKG.

Ma'ana indai za a tsaya tsakani da Allah ayiwa Shugaba Tinubu da kuma Gwamna jihar Kebbi Dr.Nasir Idris (Kauran Gwandu) aiki don su sake cin zabe a 2027 to bukatar Dan'majen Gwandu ta biya.


Wannan ne yasa lokacin da aka sanar da kirkiro da TKT, Kai tsaye DAN'MAJEN GWANDU Ya tashi ya bada gudumuwar sa Naira miliyan 100 (N100million) wannan kyautar ta dambala lissafin masu boyayya manufa akan kirkiro da TKT, kuma wannan kyautar ya nuna KWAREWAR DAN'MAJEN GWANDU akan harkar siyasa_ domin har yanzu ba wanda ya taba ba TKT irin wayanan makudan kudi. Kuma da wayanan kudi Naira miliyan 100 na Dan'majen Gwandu ne TKT Ke aiwatar da aikace aikacen ta.
Atakaice, ko gobe aka kirkiro da wata kungiya da suna TKT ko TTT ko KKK ko TGG Koma wane suna aka bata, ba zai shafi tafiyar TKG din Dan'majen Gwandu ba(Jami'ar Siyasar Jahar Kebbi)...Kuma a shirye Dan'majen Gwandu yake ya taimaka da kayan aiki indai da gaske ake akan yiwa Shugaba Tinubu da kuma Gwamna Jahar Kebbi Dr. Nasir Idris (Kauran Gwandu) aiki domin a sake zaben su a 2027.

Post a Comment

0 Comments