Tattaunawa Ta Musanman Da Hon. Kabiru Masama Kashi Na 1.
TATTAUNAWA TA MUSANMAN Kashi Na 1
Ina Takara ne Domin Cigaban Karamar Hukumar Gwandu
TATTAUNAWA TA MUSANMAN DA DAN TAKARAR KUJERAN DAN MAJALISA JAHA, DAGA MAZABAR GWANDU; ALHAJI KABIRU MASAMA
Jaridar Kebbi-Trust Online ta sami tattaunawa da Alhaji Kabiru Ibrahim Riskuwa Masama, Dan Takaran kujeran Dan majalisan Jihar Kebbi Mai Wakiltar Karamar Hukumar Gwandu a karkashin Tutar Jam'iyar ADC, inda ya bayyana dalilan sa na fitowa takara.
_________________________________
Kebbi-Trust: Hon. Kabiru Masama, masu karatu zasu so suji takaitaccen tarihinka.
Hon. Kabiru Masama: Alhamdulillah, na gode da wannan damar da Kebbi-Trust ta bani.
An haife ni a garin Masama dake Karamar Hukumar Gwandu, nine babban Dan Marigayi Hon. Alhaji Ibrahim Riskuwa Masama. Bayan karatun firamare da Sakandare, nayi Diploma a 'Public Administration ' a Waziri Umaru Federal Polytechnic, Birnin Kebbi. Sannan naje Jami'ar Usman Danfodiyo dake Sokoto nayi Digiri a 'Public Administration'. Sannan Kuma nayi Digiri na biyu (watau Masters Degree) a 'International Affairs And Diplomacy' duk a Jami'ar Usman Danfodiyo dake Sokoto.
Nayi aiki a matakin jiha da matakin Gwamnatin Tarayya da Kuma kungiyoyi masu zaman kansu watau NGOs. Wannan ya bani damar fahintar yadda ake jagorancin jama'a.
Kebbi-Trust: Hon. Kabiru Masama mene yaja hankalinka zuwa siyasa?
Hon.Kabiru Masama: Jama'a,.. baya ga haka, na gaji siyasa daga mahaifi na, Wanda ya barmini wasiyar cewa duk lokacin da jama'a suka nemi da yin wani aiki ko takara don taimaka masu, toh in amsa kira. Yanzu jama'a sunce in fito, kuma na amsa kira.
Kebbi-Trust:Mafi yawan Yan siyasan Gwandu suna jam'iyar APC, me yasa ka zabi ADC maimakon APC?
Hon. Kabiru Masama: Kamar yadda na fada tun farko, da ra'ayin jama'a ta ce nike aiki, su suka bada shawaran ayi sabuwar tafiya ADC, Kuma na amsa kira. Domin a ADC ne muke da tabbacin samun damar yi wa jama'a aiki
Kebbi-Trust:Mafi akasarin wayanda ke kan kujeran siyasa a Gwandu, kamar iyaye ne a gareka, me yasa zaka nemi yin takara da su?
Hon. Kabiru Masama: Kundin tsarin mulkin Najeriya ne ya bani damar yin takaran dukkan kujeran da nike bukata. Na biyu a al'ada ta Hausa-Fulani, idan uba na kan aiki, sai karfin Dan sa ya kawo, to wajibi ne Dan ya taimaka ya amshi aikin don ya hutar da uban nasa.
A matsayina na Da Mai ladabi da biyayya, na fito ne don in ba Baba dama yaje gida ya huta, ya barmu da wannan aikin Mai matukar wahala.
_______________________
_A Kashi na 2 na wannan tattaunawa, zamu ji alakar Hon. Kabiru Masama da tsohon Ministan Shari'a Abubakar Malami SAN da Kuma ra'ayin sa akan matsin lambar da yake sha daga manyan mutane inda suke rokon sa da yajaye takaran sa...da sauran Karin bayani akan Shirin da yayi wa wannan sabuwar tafiya ta ADC_ .

Post a Comment
0 Comments