KANTOMA:. KAURAN GWANDU YA YI ADALCI A DANDI

KANTOMA:  KAURAN GWANDU YAYI ADALCI A DANDI

NADA DR.MANSUR ISA KAMBA A MATSAYIN SHUGABAN RIKO  NA KARAMAR HUKUMAR MULKI TA DANDI YA TABBATAR DA MAI GIRMA GWAMNAN JIHAR KEBBI DR. NASIR IDRIS (KAURAN GWANDU) ADALI NE KUMA MAI SAURAREN KORAFIN JAMA'A NE

By Ahmad Umar

Mai girma Gwamnan Jihar Kebbi Dr Nasir Idris (Kauran Gwandu) ya nada Dr. Mansur Isah Kamba a matsayin Shugaban riko na karamar hukumar Mulki ta Dandi.

Wannan nadin ya farantawa mutanen karamar hukumar Dandi rai, kasancewar Dr. Mansur ya bautu a Siyasar Dandi ba tare da an saka masa ba, sai yanzu da Allah Ya kawo adalin Gwamna Mai sauraren korafin jama'a.
Wannan jaridar ta Kebbi-Trust tayi wallafe wallafe da dama akan rashin adalcin da akayi wa wannan bawan Allah a baya a Siyasar karamar hukumar Dandi.

Karamar Hukumar Dandi Babban Tunga ce ta manyan kusoshin jam'iyar PDP dake da makudan kudade a hannun su, amma a haka Dr. Mansur Isah baya rike da kowane irin mukami na gwamnati, ya dinga zuba dukiyarsa yanawa APC aiki har aka sami nasara akan PDP.

Bayan haka a tarihin Siyasar Dandi Dr. Mansur ne kawai ya taba anfani da dukiyarsa wajen gina al'umma kamar haka:

- Ya gina makaranta akan kudi sama da N10million don Ya'ya talakawa su sami ilimi kyauta
- Ya gina rijiyoyin bultsatse
- Daga 2012 zowa yau ya raba JAMB Forms sama 1,000 kyauta. Wasu da suka anfana sun gama jami'a wasu Kuma cikin karatun
- Tsakanin Arewa da Dandi yasa an koyawa mata da Matasa sama da 1,000 sana'o'in hannu kyauta
- Ya raba littafai sama da 10,000
- Ya raba magunguna a asibitoti dake fadin Dandi kyauta da sauran su.
A zaben Gwamna a 2023 Dr. Mansur  ya ba jam'iyar APC gudumuwar sabbin mototi guda biyu.
Sannan cikin su 4 da suka jagoranci kai APC a samun nasara  a zaben 2023 shine kawai ba sakawa ba.

1- An sakawa Hon. Garba Rabi'u Kamba, yanzu shine Dan majalisan wakilai

2- An sallami Hon. Abdulsalam Jibril da kujeran local government chairman.

3- An sakawa yan' kungiyar 9 wards da mukamin 'Commissioner', 'Member State House of Assembly' , E.S, SSA, Chairman Party da sauran su

4- Dr. Mansur ne dama yayi saura: Wannan ne dalilin da yasa mutanen Dandi suka yabawa  Mai girma Gwamnan Jihar Kebbi Dr. Nasir Idris (Kauran Gwandu) bisa wannan tunani da hangen nesan da ya nuna nayiwa wannan dan talkin, Dr. Mansur adalci ta hanyar nada shi kantoman karamar hukumar mulki ta Dandi.
 Ana Kuma kyauta zaton Dr. Mansur ne zaiyi takaran Chairman na Dandi a karkashin jam'iyar APC In sha Allah.

Da fatar Dr. Mansur Isah Kamba zai ba marada kunya, ta hanyar ci gaba da ayukkan alheri da ya saba yi da kudin aljihun sa ballantana yanzu ga tallafin kudin gwamnati.
______________________________
07038182929

Post a Comment

0 Comments