TA BARE TSAKANIN SEN. ALEIRO DA SEN.YAHAYA, KOWA YA KAMA GABAN SA

TA BARE TSAKANIN SEN. ALEIRO DA SEN. YAHAYA, KOWA YA KAMA GABAN SA

Sanata Adamu Aleiro da Sanata Yahaya Argungu sun kawo karshen auren zoben siyasa da ke tsakanin su, inda kowa ya kama gaban sa.

Yayin da mafi akasarin abokan tafiyar Aleiro suka koma jam'iyar PDP, babban jigon tafiyar Sanata Yahaya yace Allah Ya raka taki gona ya na nan a jam'iyar sa ta APC.

Abin tausayi shine yadda Sanata Yahaya yayi ta Maza ya sayi form din takaran Gwamna a APC duk da masaniyar da yake da ita cewa baida delegate ko daya.

Tun farko mutane sunyi mamakin yadda Mallamawan Kebbi yayi watsi da akidar da aka san shi da ita, inda da rana tsaka ya mayar da kansa yaron Sanata Adamu Aleiro.

Kasancewar siyasar bangaren Adamu Aleiro ta shiga rudani inda wasu suka koma PDP, wasu sukabi Gwamnati wasu kuma har yanzu sun kasa yi wa kansu matsaya.

Cikin wannan hayagagan ne shi kan Sanata Yahaya ya zabi zama a APC tare yin ta Maza ya sayi form din takaran Gwamna a APC.

Amma ana ganin kamar gudumuwar kudi ne kawai yaba APC ta hanyar sayen form la'akari da cewa baida delegate ko daya idan anzo taron fidda gwani.

Post a Comment

0 Comments