Politica
Malami ya ba yan 'social media' din sa mamaki
Malami yayi wa yan 'social media' ruwan kudi
Ranar Jama'a 29/4/2022 ba zato ba tsanmani yan social media din Ministan Shari'a Abubakar Malami sun waye gari suka ga N50,000 kwance a cikin asusun ajiyar su na banki.
Abin birgewa shine yadda Shugabannin yan social media irin su Malam Ahmad Khadimiyya suka dinga sanarwa cewa duk Wanda baiga kudin a Account din sa na banki ya tuntube su domin ganin kowa ya sami kudin sa kai tsaye.
Kasancewar wannan alheri yazo bazata ya farantawa yan 'social media' din gidan minista rayuwa inda suka tayi masa luguden yabo.
Idan za a tuna a ranar Alhamis 28/4/2022 a taron Shugabannin APC na jahar Kebbi tun daga matakin wards da matakin karamar hukuma da matakin Jiha sai da Minista Abubakar Malami ya bisu daya bayan daya da N20,000 wasu kuma N30,000.
Malami yayi wayannan hidimomin ne kasa da sati biyu da yayi ruwan shinkafa da gero a jahar Kebbi Wanda ba wani dan siyasa a Jihar Kebbi da ya taba yin irin wannan hidimar.

Post a Comment
0 Comments