Tarihin Dan'Majen Gwandu Kashi Na 5 (Ilimin Dan'Majen Gwandu)

ASAN MUTUM; ASAN HALIN SA; ASAN AIKIN SA : SHARHI AKAN RAYUWAR DAN'MAJEN GWANDU

   ( Kashi Na 5)
ILIMIN DAN'MAJEN GWANDU 

Daga Ahmed Umar 
Sanin mutum da sanin halin sa da kuma sanin aiki sa, sune ma'aunin hankali da mutane ya kamata suyi la'akari da su wajen ma'amala ta yaro da uban-gida da  kuma wajen zaben shugabanni.

A wannan kashi na 5, akan sharhin tarihin Injiniya Ahmad Umar Farouk (Dan Majen Gwandu, Gamjin Kabi) Kuma Shugaban Hukumar Kula da Sararin Samaniya na Nijeriya (watau MD, Nigeria Airspace Management Agency 'NAMA') zamuyi takaitaccen bayani akan Karatu ko Ilmin sa In Sha Allah.



1-WANE NE INJINIYA AHMED UMAR FAROUK (DAN MAJEN GWANDU)? kashi na 5::  ILIMIN DAN'MAJEN GWANDU 


 Allah Ya taimaki Injiniya Ahmed Umar Farouk da yin Karatu mai zurfi kuma mai Albarka.
Wannan nasarar ta samu ne bisa tarbiyar da ya samu daga iyaye sa da kakannin sa masu albarka.

Kamar Dan'uwan sa Marigayi Sir. Ahmadu Bello (Sardaunan Sokoto), Allah Ya ba Injiniya Ahmed Umar Farouk ilimin addinin musulunci da ilimin zamani (boko); wannan ilimin addinin da ya samu ne ya haskaka zuciyar sa yake koyi da Sayyidina Abubakar wajen yin alheri, kyauta da sadaka  da kuma shawan daukar nauyin karance karancen addinin musulunci a kafafen yada labarai da dama a Jihar Kebbi
Bayan ilmin addini da na firamare, Dan'Majen Gwandu ya sami ilmin sakadare a makarantar sakadaren Gwamnati ta kimiya dake Birnin Kebbi da yanzu ake kira 'NAGARI COLLEGE', Birnin Kebbi inda ya karanci darussan kimiya ( watau Chemistry, Physics, Biology, Mathematics da sauran su) ya kammala a 1988.

Dan'Majen Gwandu ya karanci Difoloma a fannin Injiniya (Diploma Mechanical Engineering') daga nan sai ya shiga Jami'ar Fasaha dake Minna, Jahar Niger (Federal University of Technology, Minna) Inda ya karanci Digiri a fannin Injiniya (B.Eng. 'Mechanical Engineering' Second Class Upper Division').
Dan'Majen Gwandu ya samu Digiri na biyu (Masters Degree) har guda biyu: 

-Na farko ya karanci Digiri na biyu  a fannin kasuwanci (Masters Degree in Business Administration) daga Jami'ar Jihar Lagos;

-Sai Digiri na biyu a fannin Harkokin kasashen waje (Masters Degree in International Affairs and Diplomacy) daga Jami'ar Ahmadu Bello dake Zaria. 

Dan'Majen Gwandu ya kuma  karanci babban Difoloma  a fannin Sarrafa kudi (PGD, Financial Management) daga Makarantar Hurar da Kwararrun Ma'aikata (Chartered Institute of Administration, Lagos)

Wannan ne dalilin da yasa idan kaji Dan'Majen Gwandu na buga Turanci zaka zaci gidan Sarauniyar Ingila ne aka haife shi.

Dan'Majen Gwandu Yayi Karatu, kuma Allah Ya albarkaci karatun sa; yan'uwa, makwabta, abokan aiki, abokan karatu (classmates), hadiman sa da sauran su, shaidu ne akan alheri da kyauta da Allah Ya albarkaci rayuwar Dan'Majen Gwandu da su.

 Mu hadu a kashi na 6 domin ci gaba

( A kashi na gaba zamuyi bayani akan iyalan Dan'Majen Gwandu da kuma aikace aikacen sa har zuwa matsayin sa na 'MD, Nigeria Airspace Management Agency 'NAMA'' In Sha Allah) 


2- MENE NE HALAYAN INJINIYA AHMED UMAR FAROUK (DAN MAJEN GWANDU)? 

 Gaskiya, rikon amana da so da kaunar jama'a sune halayar Dan'Majen Gwandu


3- MENE NE AYUKKAN INJINIYA AHMED UMAR FAROUK (DAN MAJEN GWANDU) ?

 Bautan Allah, Alheri, Kyauta,  da Tausayin bayin Allah sune ayukkan Dan Majen Gwandu

____________________
Ahmed Umar 
Publisher Kebbi-Trust Online Newspaper 
ahmadugamji@gmail.com 
07038182929

Post a Comment

0 Comments