Sulhu Tsakanin Manoma Da Makiyaya A Dandi

*SHUGABAN KARAMAR HUKUMAR DANDI DR.MANSUR ISAH YA KAWO KARSHEN RIKICIN SHEKARU SAMA DA 30 TSAKANIN MANOMA DA MAKIYAYA A GARIN FINGILLA*


Shugaban karamar hukumar Mulki ta Dandi Dr Mansur Isah Kamba (PhD) cikin hukuncin Allah Ya sami nasaran warware tsohowar rikici ta sama da shekaru 30 a tsakanin fulani makiyaya da mutanen gari manoma  dake cikin garin Fingilla.
Bayan ya saurari ko wane bangare sai ya tashi da Kansa yaje tsakiyar dajin da ake yawan samun sabanin domin shaida abinda ko wane bangare ya fada.
Dr. Mansur ya gabatar da shawarwari sa ga dukkan bangaro dake rikici da juna inda ko wane bangare yayi ma'am da shawarwari da aka gabatar tare da alkawalin kiyaye dukkan sharuddan da aka zayyana.
A karon farko anga wasan barkwanci tsakanin bangarorin biyu abinda ke nuna an sami fahintar juna a tsakanin bangarorin biyu.
Dr. Mansur yayi anfani da wannan damar wajen sanar da kokarin da mai girma Gwamna Jihar Kebbi Dr Nasir Idris Kauran Gwandu keyi wajen taimakawa dukkan manoma da makiyaya, inda yayi kira gare su da suci gaba da ba Gwamnati goyon baya da hadin kai domin cimma wayannan manufofin.

Post a Comment

0 Comments