Shugabanci Da Shawaran Dattawa A Dandi
AIKI DA HANKALI: Shugaban Karamar Hukumar Dandi Dr Mansur Isah Ya Kafa Kwamitin Dattawa 55 Da Zasu Dinga Bashi Shawara Akan Tafiyar Da Mulkin Dandi*
A karon farko a tarihin shugabancin Karamar Hukumar Dandi, Shugaban Karamar Hukumar Dr. Mansur Isah ya kafa Kwamitin Dattawa 55 domin taya shi tafiyar da mulkin karamar hukumar.
Dr. Mansur yace ya kafa wannan kwamiti ne domin su bashi shawara akan yadda za a kai karamar hukumar Mulki ta Dandi ta samu ci gaba har ta tserewa tsara.
Dattawan da suka hada da manyan malaman addini, Yan kasuwa, manyan Yan Boko da Yan siyasa, manyan sojoji, Yan sanda da sauran su; sun nuna Jin dadinsu da yadda Dr. Mansur ya mutunta su ta hanyar neman shawaran su don haka sunyi alkawalin yin dukkan mai yiwuwa wajen ganin ya Sami nasara a shugabancin ta hanyar bashi shawarwari na gari.
Kwamitin dai an rabashi gida biyu; watau kwamitin Dattawa da ya kunshi dattijo 55, da Kuma kwamitin ma'aikatan Gwamnati da zabanbun Yan siyasa su 15.
Mafi akasarin dattawan sunyi jawabi mai gamsarwa a wajen taron tare da alkawalin bayarda shawarwari masu ma'ana da zasu kawo ci gaba a karamar hukumar Mulki ta Dandi.
Da karshe an zabi Alhaji Habib Muhammad Sabi Kamba Sakataren dim-dim (permanent Secretary) kuma shugaban filin jirgin sama na Sir Ahmadu Bello dake Birnin Kebbi a matsayin Shugaban wannan kwamitin tare da Col. Muhammad Dole (Rtd) a matsayin secretary na kwamitin.
Kadan daga cikin dattawa 55 da Zasu dinga baiwa Dr. Mansur shawara sun hada da Mai girma Sarkin shiko Muhmud Z. Fana,Hon. Garba Rabi'u Kamba, Hon. Sulaiman Fana, Sheikh Shu'aibu Abdulrazak, Sheik Malam Dan misira, Ambassador Sani Dole, Prof. Ahmad Kyangakwai, Retired DSS Director, Sanusi Kamba, Alhaji Makera Kyangakwai, Hon. Nura Fingilla, Dr. K.K, ACGNIS, Ango Fana(Rtd), Alhaji Dan dare Boss, Hon. Garba Fana da sauran su.
Dr. Mansur yayi alkawalin aiwatar da dukkan shawarwarin da zasu bashi domin ci gaban karamar hukumar Mulki ta Dandi.
Post a Comment
0 Comments