ZABE A YAURI/SHANGA DA NGASKI -2024

CIKE GURBI A YAURI/SHANGA DA NGASKI


ZABEN CIKE GURBI A MAZABAR YAURI/SHANGA DA NGASKI: DR. SUNUNU YABAR BAYA DA KURA: 

____ Rikici Ya Barke A Jam'iyar PDP

___Sulhu Ya Watse A Jam'iyar APC,..Gwamna Yace baida Dan- Takara

____Hon. Halima Hassan Tukur Yauri ta Janye daga Takara
Tun lokacin da hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa INEC ta sanar da 03/02/2024 a matsayin ranar da za tayi zaben ciki gurbi na majalisar wakilai a mazabar Yauri/Shanga da Ngaski ake ta dauki ba dadi a tsakanin manyan Jam'iyun APC da PDP, Inda dukkan Yan takara a wayannan Jam'iyun kowa yayi tsayin gwamin jaki cewa in ba shi ba to sai dai a fasa kowa ya rasa.

RIKICI A JAM'IYAR PDP

Jaridar Kebbi-Trust ta sami labarin cewa mutane 6 ne suka tsaya takara a jam'iyar PDP da suka hada da Hon. Hassan Warra, Hon. Shehu Na Tsaffi, Alhaji Bashar Dan malikin Saminaka da sauran su.

Tashin farko Yan takaran sun amince da yin sulhu domin tsayar da mutun daya a tsakanin su.

YADDA SULHUN YA KASAN CE

Majiyar mu ta farauto cewa da farin Yan takaran su 6 sun amince da su kada kuri'a su zabi mutum daya, Inda Hon. Hassan Warrah ya Sami kuri'u 3 shi Kuma Alhaji Bashar Dan malikin Saminaka ya Sami kuri'u 2, Amma sai yayi fatali da wayannan kuri'un Inda ya nuna cewa warnuwa ce akayi masa. Jin haka sai sauran Yan takaran sukace amaida gami, ayi watsi da sulhun aje ayi 'prmary election ' duk Wanda Allah Ya ba a bishi, yanzu a haka ake a PDP.

SULHU YA WATSE A APC

Itama jam'iyar APC duk kokarin da akayi domin a sasanta Yan takara su sama da 10 abin ya cutura.

Har da hikamar da akayi na anfani da Malaman addini Inda suka ta kwarara masu ayoyin Alkur'ani da Hadisan manzon Allah aka samun Mulki da rashin samu; Amma bayan Hon. Halima Hassan Tukur ba Wanda ayar ko hadisi ya ratsa a cikin Yawurawan, Inda ko wanen su yaja daga in bashi ba ta fashe.

Yanzu dai Mai Girma Gwamnan Jihar Kebbi Dr. Nasir Idris (Kauran Gwandu) yace a kyale su suje suci kansu tunda ayoyi da hadisai sun kasa tasiri akan su.

HON. HALIMA HASSAN TUKUR YAURI TA JANYE TAKARAN TA

Wa'azin da Malaman suka share yini sunawa Yan takara ya ratsa Hon. Halima Inda tace ita kan tabarwa ALLAH Komai, ta janye takara, don a Sami zaman lafiya a jam'iyar APC kamar yadda Mai girma Gwamna ke muradi.

GWAMNA YA YIWA HON.HALIMA LUGUDEN YABO, YA BATA MAKUDAN KUDI DA MUKAMI KAI TSAYE TARE DA ALKAWALIN BATA WANI MUKAMIN A NAN GABA

Jin dadin yadda Hon. Halima Hassan Tukur Yauri ta nuna dattako ta hanyar janyewa ya birge 'His Excellency' Inda Kai tsaye yace a mayar mata da dukkan kudaden da ta kashe, sannan ya umurci daga yau a ci gaba da biyan ta Albashin SSA Mai Babban riga da rawani, kafin yayi tunanin mukamin da zai bata a nan gaba, ko a matakin tarayya ko a matakin Jaha.

Don haka a takaice ana iya cewa Hon. Halima Hassan Tukur Yauri ta lashe zabe, domin Gwamna yace an rufe kofar alkawalin mayar wa Dan takara kudin sa da Kuma bashi mukami da akayi tun farko ga dukkan Wanda ya jaye takaran sa, yanzu duk Dan takaran da ya fadi zaben fidda gwani (primary election) TSULA ZAI TASHI.

Dukkan Jam'iyun APC da PDP a ranar Asabar 6/1/2024 ne ranar da zasu gudanar da zaben fitar da gwani (primary election).

Yawurawa sun sa Ido suga wayanda da Jam'iyun APC da PDP zasu tsayar takara domin maye gurbin da Dr. Tanko Yusuf Sununu ya bari.

Post a Comment

0 Comments