Tarihin Dan'majen Gwandu (Kashi Na 9)

ASAN MUTUM; ASAN HALIN SA; ASAN AIKIN SA : SHARHI AKAN RAYUWAR DAN'MAJEN GWANDU

           ( Kashi Na 9)


YADDA SHUGABA BUHARI DA WASU KUNGIYOYI DA DAMA SUKA KARRAMA DAN'MAJEN GWANDU

Daga Ahmed Umar 


Sanin mutum da sanin halin sa da kuma sanin aiki sa, sune ma'aunin hankali da mutane ya kamata suyi la'akari da su wajen ma'amala ta yaro da uban-gida da  kuma wajen zaben shugabanni.

A wannan kashi na 9, akan sharhin tarihin Injiniya Ahmad Umar Farouk (Dan Majen Gwandu, Gamjin Kabi) Kuma Shugaban Hukumar Kula da Sararin Samaniya na Nijeriya (watau MD, Nigeria Airspace Management Agency 'NAMA') zamuyi takaitaccen bayani akan lambobin yabo da ya samu tun lokacin mulkin shugaba Buhari da Kuma wayanda ya samu a wannan mulki na Shugaba Tinubu.


1-WANE NE INJINIYA AHMED UMAR FAROUK (DAN MAJEN GWANDU)? kashi na 9:

 Allah Ya albarkaci Dan'majen Gwandu da Ilimi da iya shugabanci da kwazo da bisira, wayannan baiwan ne suka sa ya sami karramawa da lambobin yabo da dama kamar haka:

- Lambar yabo daga fadar Shugaba kasa(watau National Productive Order of Merit(NPOM) wadda Shugaba Buhari ya bashi a lokacin mulkin sa.
- Dan'majen Gwandu ya sami lambar yabo daga kungiyar injiniyoyi ta Najeriya( watau Fellowship of the Nigeria Society of Engineers 'FNSE' award)

- Dan'majen Gwandu ya sami lambar yabo da kungiyar injiniyoyi fannin kanikancin mototi ( watau Fellowship of the Nigeria Institute of Mechanical Engineers (FNiMechE) award

- Dan'majen Gwandu ya sami lambar yabo daga hukumar kwararru akan mulki ( watau Fellowship of the Chartered Institute of Chartered Administrators 'FCIA' award)

- Dan'majen Gwandu ya sami lambar yabo daga hukumar kwararrun injiniyoyi (watau Fellowship of the Nigeria Institute of Safety Engineers 'FISE' award)

- Dan'majen Gwandu ya sami lambar yabo daga kungiyar tabbatar gaskiya a ayukkan gwamnati ( watau Better Nigeria Fellowship Award  for Exemplary Public Seevice) da sauran su

Baya ga wayannan lambobin yabo, sarakuna da dama sun hangi bisiran da Allah Yayi wa Dan'majen Gwandu don haka sai Suma suka bashi sarautar garjiya a masarautun su, kamar haka:

-"Dan'majen Gwandu" karramawa daga Masarautan Gwandu 

-"Gamjin Kabi" karramawa daga Masarautar Argungu 

-"Wazirin Dalijan" karramawa daga Masarautar Dalijan 

-Matawallen gabas da sauran su.

 Mu hadu a kashi na 10  : A kashi na gaba watau Kashi na  10, zamuyi karin bayani akan wasu jarumtaka da basira da Allah ya horewa Dan'majen Gwandu.


2- MENE NE HALAYAN INJINIYA AHMED UMAR FAROUK (DAN MAJEN GWANDU)? 

 Gaskiya, rikon amana da so da kaunar jama'a sune halayar Dan'Majen Gwandu

3- MENE NE AYUKKAN INJINIYA AHMED UMAR FAROUK (DAN MAJEN GWANDU) ?

 Bautan Allah, Alheri, Kyauta,  da Tausayin bayin Allah sune ayukkan Dan Majen Gwandu


____________________
Ahmed Umar 
ahmadugamji@gmail.com 
07038182929

Post a Comment

0 Comments