Zaben Cike Gurbin A Mazabar Yauri- 2024

Siyasar Yauri/Shanga/Ngaski 2024


An Bankado Yunkurin Tafka Magudi Da Zai Iya Kawo Tashin Hankali Da Tarzoma A Kasar Yauri

___Daya daga cikin yan takara yayi yunkurin kafa 'delegates' shi kadai

___Jam'iyar APC Matakin Jaha Tasha Alwashin Mummunan Hukunci Ga dukkan Dan takaran Da Yayi Yunkurin Nada 'Delegates' domin cutar da sauran Yan takara

___ Tuni Yan Takara 8 Sun Sayi 'Form'

Shawar da jaridar Kebbi-Trust keda shi a zaben cike gurbi da za a gudanar a mazabar Yauri, Shanga da Ngaski a watan Fabairu 2024, yasa jaridar lekewa a babban ofishin jam'iyar APC na kasa domin sannin abinda ake kullawa.

Kuma cikin nasara mun samo labaru masu dama da zamu sanar da Yawurawa domin kaucewa zaben tumun dare.

DOKOKIN HUKUMAR ZABE TA KASA (INEC) AKAN ZABEN CIKE GURBI A MASARAUTAR YAURI

Hukumar zabe ta kasa (INEC) ta sanar da ranar sayen form na Yan takara da Kuma form na takaran delegates daga 27/12/2023 zuwa 02/01/2024. 

A sabon dokokin zabe ( Electoral Act) Exco basuda hannu wajen fitar da yan takara (Primary Election), delegates ne ke da wannan damar, kuma mutum bai zama delegates sai ya sayi form shima yayi takara an zabe shi a matsayin delegates din.

An sanya 03/01/2024 a matsayin ranar mayar da form da Yan takara majalisa da Yan takaran delegates suka cike.

05/01/2023 za ayi zaben delegates, in gari ya waye kuma watau 06/01/2024 sai delegates din da aka zaba su kuma su zabi Dan-Takara (Primary Election).


YUNKURIN TAFKA MAGUDI DA ZAI IYA KAWO TASHIN HANKALI
Fahintar wannan tsarin ne yasa daya daga cikin yan takaran kujeran majalisan wakilai da a za a gudanar, yayi yunkurin sayen forms na delegates da niyar rabawa magoya bayansa don idan anzo zaben fitar da gwani(primary election) sai su zabe shi su Kuma sauran Yan takaran a rubuta masu ZIRO.

A sabon dokokin zabe, ko wace karamar hukuma za a zabo delegates 50 ne, a mazabar Yauri Shanga da Ngaski ana maganar delegates 150 kenan.

Majiyar Kebbi-Trust ta gano cewa shi wancan dan takaran ya biya ko yayi niyar biyan kudin forms din delegates 150 da niyar saka su cikin aljihun sa shi kadai, Wanda yin haka zai iya kawo yamutsi da tarzoma idan ba a taka mashi birki ba, domin sauran Yan takaran ba zasu zuba ido ba ayi masu sakiyar da ba ruwa.

Ko a zaben gama gari na 2023 shi wannan dan takaran dake rike da mukamin shugaban karamar hukuma (Local Government Chairman) shine kanwa uwar gamin badakalar da tasa aka soke zaben farko na fitar da gwani Inda aka sake Karo na biyu, Allah Ya ba Dr. Tanko Yusuf Sununu nasara, sabanin Hon. Umar Uba (Bullet) da shi shugaban karamar hukuma ke marawa baya a wancan lokacin.

UWAR JAM'IYAR APC TA JAHAR KEBBI TACE, ITACE KE DA HURUMIN SAYE DA SAYAR DA FORMS DIN TAKARAN DELEGATES. KUMA DUK WANI DAN TAKARA DA YA SAYI FORMS DIN DELEGATES ZA A HUKUNTA SHI.

Kebbi -Trust ta tuntubi kakakin jam'iyar APC na Jaha, akan ko Dan -takara na da damar sayen form din delegates don rabawa magoya bayansa don ya mamayi sauran Yan takara?

Kakakin APC ya tabbatar wa Kebbi-Trust cewa jam'iya ce kawai keda iKon saye da sayar da form din takaran delegates, Kuma duk Dan takaran da ya nemi cutar da Yan uwansa ta hanyar sayen delegates form za su hukunta shi.

YAN TAKARA 8 NE SUKA SAYI FORMS

Kebbi-Trust ta gano cewa ahalin yanzu Yawurawa 8 ne suka sayi forms domin neman maye gurbin da Dr. Sununu ya bari.

Yan takara 8 sun hada da Hon. Halima Hassan Tukur Yauri; Dr. Jibril Abubakar Abarshi; Hon. Sani Yusuf Rukubolo; Hon. Bala Muhammad (Gagga); Hon. Umar Uba, Prof. Aliyu Yauri, Hon. Rilwanu Abarshi da sauran su

Talata 02/01/2024 ne rana na karshe na sayen form, sannan Kuma ranar Larba 03/01/2024 ne rana na karshe na mayar da form din da aka saya.

Idan an sami sulhu, ba za'ayi primary election ba, idan kuma sulhu ya gagara za ayi primary election a 06/01/2024.

Post a Comment

0 Comments