Siyasar Yauri/Shanga Da Ngaski -2024

YAURI/SHANGA/ NGASKI -2024


YAU ASABAR 6/1/2024 APC ZATAYI ZABEN FIDDA GWANI (PRIMARY ELECTION):..Yan Takara 9 sunyi koyi da ya'yar su Kuma Malamar Siyasar su Hon. Halima Hassan Tukur Yauri; Sun janye takara,........ko APC zata karbi shahadar su, kamar yadda aka karbi shahadar Malamar su Hon. Halima Hassan Tukur Yauri?

Dukkan Yan takaran APC sun janye daga takara in banda mutane 3, don haka za a fafata a tsakanin su:

Yan takara ukkun da sukaki jayewa juna da Za a fafata tsakanin su, sune:

1- Hon. Umar Uba (Bullet)) da Gwamnati ke marawa baya

2- Dr. Jibril Abubakar Abarshi da ake hasashen Minista ilmi ke goyawa baya.

3- Hon. Sani Yusuf Rukubolo; Dan takara mai zaman Kansa 

Kebbi-Trust Online Newspaper zata kawo maku yadda ta kaya, InshaAllah

ALLAH YA BA MAI RABO SA'A 

Post a Comment

0 Comments