RAMADAN: Malami Yayi Abinda Ya Saba

JAKADAN ARZIKI GA AL'UMMAR JAHAR KEBBI ABUBAKAR CHIKA MALAMI YA RABA BUHU 17000. NA ABINCI DON SAMUN SAUKIN AZUMI NA 2022.

By Abubakar Kamba
Malami Drum Beats

Mai girma Ministan sharia Abubakar Chika Malami ya rabawa kananan hukumomi guda 21 dake fadin wannan jaha  buhu 17000 na abinci kama daga gero dawa da kuma shinkafa don samun saukin gudanar da azumin watan Ramadana na wannan shekara. 

Ministan shari'a Abubakar Malami lokacin da yake gabatar da jawabinsa a wajen wannan taron da aka gudanar a filin wasannin na Haliru Abdu da ke Birnin Kebbi  ya samu halartar manyan yansiyasa, shugabanin addini, matasa da kuma kungiyoyin mata na ciki da wajen jahar kebbi. Ministan ya yi godiya ga Allah subhanahu wata'ala da ya haɗa tarayyarsa da ta shugaban kasa Muhammadu Buhari, da ta Gwamna Sen. Abubakar Bagudu da kuma jam'iyar APC wajen tafiya kan wanzarda shugabanci na gari a tsakanin al'umma.

Harwayau, a wajen taron Maigirma Ministan Shari'ah ya yi kira ga masu hannu da shuni na wannan jaha da kuma Najeriya da su dage wajen taimakawa jama'a da kayayyakin abinci don samun gudanar wannan azumi chikin sauki da kuma walwala. 

Wani abin burgewa a wajen wannan taron shine irin yadda aka tsara manyan motoci masu ɗaukar kaya su ka ɗauki kayan kowace karamar hukuma da ke fadin wannan jaha suka kai mata. 

Sau da yawa yansiyasa na raba kayan azumi amma Abubakar Malami ya shiga tarihi wajen bayarda kayan azumi mafi yawa kuma cikin tsari da kuma mutanta mutanen kowace karamar hukuma a jahar Kebbi.

Abubakar Kamba
Malami Drum Beats

Post a Comment

0 Comments