Politics
YANZU YANZU: ATIKU BAGUDU YA AMINCE DA TAKARAR MALAMI
ATIKU BAGUDU YA AMINCE DA TAKARAR MALAMI
Daga: AHMAD UMAR
A yanzu ta tabbata cewa Gwamnan Jihar Kebbi Abubakar Atiku Bagudu ya amince da takarar Ministan Shari'a Abubakar Malami a zaben 2023.
Wannan bayanin ya fito filine a taron bayarda kayan azumi da Abubakar Malami ya bayar a ranar Asabar 9/04/2022 a filin wasa na Haliru Abdu dake Birninkebbi.
Irin yadda kanana, matsakaita da kuma manyan yaran Gwamna Atiku Bagudu suka cika wajen taron kawai ya isa ya gamsar da kowa cewa an dandale tsakanin Atiku Bagudu da Abubakar Malami.
Kalaman da wakilin Gwamna kuma Sakataren Gwamnatin Jiha, Alhaji Babale Umar yayi a wajen taron su suka tabbatar da cewa a 2023 Malami ne sak.
Lokacin da ya ke jawabi a madadin Gwamna bayan ya ambaci sunan Malami a matsayin Ministan Shari'a na Nijeriya sai kuma yace '' Gwamnan jiha a 2023 InshaAllahu.."
Sanin irin taka tsantsam da Babale Umar keda shi a alakar sa da Gwamna ba zai yi wannan kalamar ba idan gemu da gemu ba su hadu ba. Kuma wannan kalamar sun tabbatar da cewa Gwamna Atiku Bagudu ya amince ya marawa Abubakar Malami a takaran Gwamna a 2023.
Kadan daga cikin hadiman Gwamna Atiku Bagudu da suka halacci taron suka kumayi luguden yabo ga Abubakar Malami sun hada da P.A Faruku Enabo, Alh. Faruku kuro, SSG Babale Umar Yauri da sauran su.
Sauran manyan baki da suka halarci taron sun hada tsohon Gwamna Sa'adu Dakingari, tsohon mataimakin Gwamna Bello Dantani Argungu, Kauran Gwandu Dr. Nasir Idris, Katikan Yauri da Zaruman Mai martaba Sarkin Yauri Hon. Halima Hassan Tukur Yelwa, komishinoni da yan majalisa da sauran su.
Har ila yau matan minista Hajiya Aisha da Hajiya Fatima suma sun halarci taron.
Kimanin tirela dari (100) na shinkafa, gero da masara ne aka rabawa kananan hukomomi 21 da sauran kungiyoyi da ke jiha
Rahoto: AHMAD UMAR
Post a Comment
0 Comments