Shugaban karamar hukumar Dandi Dr. Mansur Isah ya karrama 'Class mate' din sa
Shugaban karamar hukumar Dandi Dr. Mansur Isah ya karrama 'Class mate' din sa
Shugaban karamar hukumar Dandi Dr. Mansur Isah ya karrama 'Class mate' din sa na GSS Kamba da suka kamla karatun su a shekarar 1998.
Dr. Mansur wanda kuma shine shugaban kungiyar ya nuna jin dadin sa bisa ga gudumuwar da classmate dinsa ke bashi a koda yaushe.
Anyi taron ne a ranar Asabar 10/1/2026 a dakin taro na karamar hukumar Dandi.
Membobin kungiya sun taya Dr. Mansur Isah murnar samun wannan daukaka da Allah Ya bashi tare da addu'ar Allah Ya taya shi riko.
Anyi anfani da damar wajen gabatar korafe korafen wasu membobin wannan kungiya ta GSS Kamba 1998 old boys, inda Dr. Mansur yayi alkawalin dubawa da kuma ci gaba da taimakawa dukkan Clasmate din sa.
Wasu daga cikin classmate din sunyi anfani da wannan damar wajen mika godiyar su ga Dr. Mansur bisa taimako da ya basu:
Aminu Sulaiman, ya godewa Dr. Mansur bisa taimaka masa da yayi ya sami mukamin STAFF OFFICER, na Dandi local government.
Haka ma Ahmed Umar wanda shine yayi Head Boy a GSS Kamba, 1998 da kuma Yakubu Abubakar Gabi sun godewa Dr. Mansur bisa samar masu da aiki a 'Nigeria for Women Project' da Bankin duniya ke daukar nauyi.
Bayan kammala taron, Dr. Mansur ya baiwa kowa kudin mota tare da zubawa kungiya wasu kudi a asusun ajiyar ta.
Da karshe, an ziyarci daya daga cikin membobin kungiya da Allah Ya jarabta da rashin lafiya watau Kabiru Labaran, inda akayi masa addu'ar samun lafiya.
An ci, an sha, anyi taro lafiya, an kammala lafiya. Sai kuma wata shekara idan Allah Ya kaimu.

Post a Comment
0 Comments