Kebbi-Trust Online Newspaper
ASAN MUTUM; ASAN HALIN SA; ASAN AIKIN SA : SHARHI AKAN RAYUWAR DAN'MAJEN GWANDU
( Kashi Na 4)
Daga Ahmed Umar
Sanin mutum da sanin halin sa da kuma sanin aiki sa, sune ma'aunin hankali da mutane ya kamata suyi la'akari da su wajen ma'amala ta yaro da uban-gida da kuma wajen zaben shugabanni.
Zamuci gaba da Kashi na 4 a sharhi na musanman akan rayuwar Injiniya Ahmad Umar Farouk (Dan Majen Gwandu) Kuma Shugaban Hukumar Kula da Sararin Samaniya na Nijeriya (watau MD, Nigeria Airspace Management Agency 'NAMA') domin ilmantar da al'ummar Jahar Kebbi tarihin wannan dan-baiwa da Allah Ya ba Jahar Kebbi kyauta.
1-WANE NE INJINIYA AHMED UMAR FAROUK (DAN MAJEN GWANDU)? kashi na 4
A wannan kashi na 4, akan sharhin tarihin Injiniya Ahmed Umar Farouk Dan'Majen Gwandu, zamuyi takaitaccen bayani akan yan'uwan sa In Sha Allah.
A matsayin Dan'Majen Gwandu na jika ga Sheikh Abdullahi Fodiyo; dukkan zuriyan Mujaddadi Shehu Danfodiyo, irin su Marigayi Sir. Ahmadu Bello (Sardaunan Sokoto) da Maimartaba Sultan Abubakar Sa'ad (Sarkin Musulmi dake kan sarauta)da sauran su duk yan'uwane ga Injiniya Ahmed Umar Farouk.
Amma domin takaitawa zan kawo sunayen yan'uwan sa da suka hada Mahaifi daya; watau Ya'yan Malam Umaru Raha Yarin Suru.
Atakaice Allah Ya albarkaci mahaifin Injiniya Ahmed Umar Farouk Dan'Majen Gwandu watau Malam Umaru Raha Yarin Suru da zaratan ya'ya 16 ( goma Sha shidda) da suka shahara a bangarori da dama kamar haka;
(1)Hajiya Kulu Umaru; (2) Muhammad Bello; (3) Abubakar Zaki Suru; (4)Dahiru; (5) Umaru Ango Suru; (6)Hajiya Hadiza Yar' Baba; (7) Usman Umar; (8)Hajiya Maimuna Ladi; (9) Dallatu Aliyu Giye Suru; (10) Rabi'atu; (11)Fatima Ige; (12)Hon. Abdullahi Umar Farouk Muslim(Majikiran Gwandu); (13) Muhammad Bello; (14) INJINIYA AHMED UMAR FAROUK (DAN MAJEN GWANDU); (15) Amina Umar Mama Gwandu; (16) Haliru Umar Farouk (Dan auta).
Cikin ikon Allah kusan dukkan wayannan yan'uwan Dan'Majen Gwandu da suka hada mahaifi daya, Allah Ya albarkace su da ilimi da arziki da kuma kokarin taimakawa jama'a.
Mu hadu a kashi na 5 domin ci gaba
(A kashi na gaba zamuyi bayani akan ilimin Dan'Majen Gwandu, aikace aikacen sa har zuwa wannan matsayin na MD, Nigeria Airspace Management Agency 'NAMA' In Sha Allah)
2- MENE NE HALAYAN INJINIYA AHMED UMAR FAROUK (DAN MAJEN GWANDU)?
Gaskiya, rikon amana da So da kaunar jama'a sune halayar Dan'Majen Gwandu
3- MENE NE AYUKKAN INJINIYA AHMED UMAR FAROUK (DAN MAJEN GWANDU) ?
Kamar yadda kowa ya shaida: Bautan Allah, Alheri, Kyauta, da Tausayin bayin Allah sune ayukkan Dan Majen Gwandu
____________________
Ahmed Umar
Publisher Kebbi-Trust Online Newspaper
ahmadugamji@gmail.com
07038182929

Post a Comment
0 Comments