Kebbi-Trust Online Newspaper
ASAN MUTUM; ASAN HALIN SA; ASAN AIKIN SA : SHARHI AKAN RAYUWAR DAN'MAJEN GWANDU
( Kashi Na 3)
Daga Ahmed Umar
Sanin mutum da sanin halin sa da kuma sanin aiki sa, sune ma'aunin hankali da mutane ya kamata suyi la'akari da su wajen ma'amala ta yaro da uban-gida da kuma wajen zaben shugabanni.
Zamuci gaba da Kashi na 3 a sharhi na musanman akan rayuwar Injiniya Ahmad Umar Farouk (Dan Majen Gwandu) Kuma Shugaban Hukumar Kula da Sararin Samaniya na Nijeriya (watau MD, Nigeria Airspace Management Agency 'NAMA') domin ilmantar da al'ummar Jahar Kebbi tarihin wannan dan-baiwa da Allah Ya ba Jahar Kebbi kyauta.
1-WANE NE INJINIYA AHMED UMAR FAROUK (DAN MAJEN GWANDU)? kashi na 3
A kashi na 1 da na 2 mun yi bayyani akan asalin Injiniya Ahmad Umar Farouk inda muka lissafo kakanninsa tunda daga Sheikh Abdullahi Fodiyo har zowa ga mahaifin sa Malam Umaru Raha Yarin Suru.
A wannan kashi na 3 zamuyi takaitaccen bayani akan mahaifin Dan'Majen Gwandu, watau Malam Umaru Raha Yarin Suru.
MALAM UMARU RAHA YARIN SURU
A takaice Malam Umaru Raha Yarin Suru, da kuma ake kira da suna Umaru Tille Gwandu, jikan Sheikh Abdullahi Fodiyo ne.
Baya ga haka, Umaru Raha Yarin Suru Jarumin hafsan soja ne; bayan ilimin addinin musulunci ya sami ingantaccen ilmin zamani.
Umaru Yarin Suru ya shiga aikin soja a shekara ta 1938, a lokacin ana kiran rudunar da suna British West-Africa Frontier Force, bayan Nijeriya ta samu yanci a 1960 aka canza sunan wannan rundunar sojoji zuwa Nigeria Army Force.
Bayan an dauke su an kuma basu horo a garin Ibadan sai aka tura su zuwa YAKIN DUNIYA NA 2, inda suka kamawa kasar Ingila dake mulkin Nijeriya a wancan lokacin.
Umaru Yarin Suru ya nuna jarumta a wajen yakin duniya, musanman lokacin da ya HARBO JIRGIN SAMAN Yakin abokan gaba, turawa sun yaba shi bisan wannan jarumta inda aka bashi lambar yabo.
Yarin Suru ya dawo daga yakin duniya a shekaran 1945, sannan yayi marabus daga aikin soja a shekaran 1948.
La'akari da kwarewan sa a fannin tsaro yasa a shekara ta 1956 Sarkin Gwandu na wancan lokacin Haruna Rasheed ya nada shi YARI watau maikula da gidan Yari a garin Suru (wannan ne asalin lakabin sa na Umaru YARIN SURU). Kuma ya shahara domin duk wani marasa gaskiya da ya buwaya, da zaran an kira Umar Yarin Suru zance ya kare; Misali za a iya kwatanta shi da Marigayi Ali Kwara wajen kwance lissafin marar gaskiya.
A shekara ta 1969 aka canza masa wurin aiki daga Suru zuwa Birnin Kebbi a matsayin Yari.
Yayi ritaya daga aikin Yari a shekara ta 1973 shekara daya bayan kirkiro da hukumar gidan Yari (watau Nigeria Prison Service) a 1972, daga nan sai ya koma garin Gwandu da zama
A takaice, Malam Umaru Raha Yarin Suru da-ne ga Majidadi Umaru Raha; shi kuma Majidadi Umaru Raha da-ne ga Malam Haliru Umaru (wanda yayi sarautar Raha); shi kuma Malam Haliru Umaru da-ne ga Malam Umaru Bakatara (Sarkin Gwandu na 10); shi kuma Malam Umaru Bakatara da-ne ga Ibrahim Khalilu (Sarkin Gwandu na 3); shi kuma Ibrahim Khalilu da-ne ga SHEIKH ABDULLAHI FODIYO.
Umaru Yarin Suru ya rasu a Birnin Kebbi a shekara ta 1996, Inda akayi jana'izar sa a makabartan Sojoji ta Dukku dake Birnin Kebbi.
Mu hadu a Kashi Na 4
( A kashi na gaba zamuyi bayani akan yan'uwan Dan'Majen Gwandu da sauran zuriya; ilimin sa, aikace aikacen sa har zuwa wannan matsayin nasa na MD, Nigeria Airspace Management Agency 'NAMA') da Kuma matsayin sa na Dan'Majen Gwandu In Sha Allah )
2- MENE NE HALAYAN INJINIYA AHMED UMAR FAROUK (DAN MAJEN GWANDU)?
Ba abinda ya canza..; Gaskiya, rikon amana da So da kaunar jama'a sune halayar Dan'Majen Gwandu
3- MENE NE AYUKKAN INJINIYA AHMED UMAR FAROUK (DAN MAJEN GWANDU) ?
Kamar yadda kowa ya shaida: Bautan Allah, Alheri, Kyauta, da Tausayin bayin Allah sune ayukkan Dan Majen Gwandu
____________________
Ahmed Umar
Publisher Kebbi-Trust Online Newspaper
ahmadugamji@gmail.com
07038182929

Post a Comment
0 Comments