Kebbi-Trust Online Newspaper

ASAN MUTUM; ASAN HALIN SA; ASAN AIKIN SA : SHARHI AKAN RAYUWAR DAN'MAJEN GWANDU

   ( Kashi Na 2)

Daga Ahmed Umar 
Sanin mutum da sanin halin sa da kuma sanin aiki sa, sune ma'aunin hankali da mutane ya kamata suyi la'akari da su wajen ma'amala ta yaro da uban-gida da  kuma wajen zaben shugabanni.

Zamuci gaba da Kashi na 2 a sharhi na musanman akan rayuwar Injiniya Ahmad Umar Farouk (Dan Majen Gwandu) Kuma Shugaban Hukumar Kula da Sararin Samaniya na Nijeriya (watau MD, Nigeria Airspace Management Agency 'NAMA') domin ilmantar da al'ummar Jahar Kebbi tarihin wannan dan-baiwa da Allah Ya ba Jahar Kebbi kyauta.



1-WANE NE INJINIYA AHMED UMAR FAROUK (DAN MAJEN GWANDU)?     (kashi na 2)

A kashi na farko mun bayyana cewa Injiniya Ahmad Umar Farouk jika ne ga Sheikh Abdullahi Ibn Fodiyo wanda ya assasa masarautar Gwandu Kuma Sarkin Gwandu na farko.

Munyi alkawalin yin karin bayani a cikin wannan kashi na 2.

Ga yadda karatun yake: 
Sheikh Abdullahi Ibn Fodiyo shi ya Haifi Ibrahim Khalilu (Sarkin Gwandu na 3); Ibrahim Khalilu shi ya Haifi Malam Umaru Bakatara ( Sarkin Gwandu na 10), Malam Umaru Bakatara shi ya Haifi Malam Haliru Umaru (Dan Galadiman Raha) watau Sarkin Raha wanda shi kuma ya Haifi Majidadi Umaru Labbo Raha; Majidadi Umaru Raha shi ya Haifi Malam Umaru Raha Yarin Suru: Shi Kuma Malam Umaru Raha Yarin Suru shi ne ya Haifi Injiniya Ahmed Umar (Dan'Majen Gwandu).

Atakaice jerin kakanni 5 ne kawai tsakanin Sheikh Abdullahi Ibn Fodiyo da Injiniya Ahmad Umar Farouk (Dan Majen Gwandu).

A matsayin Injiniya Ahmad Umar Farouk na babban Yarima a Gidan Sheikh Abdullahi Gwandu watau 'DAN'MAJE', muna yi masa addu'ar babban rabo da fatan Alheri.


A kashi na gaba zamuyi bayani akan ilimin sa, aikace aikacen sa har zuwa wannan matsayin nasa na MD, Nigeria Airspace Management Agency 'NAMA') da Kuma matsayin sa na Dan'Majen Gwandu) In Sha Allah) 




2- MENE NE HALAYAN INJINIYA AHMED UMAR FAROUK (DAN MAJEN GWANDU)? 

Atakaice, Gaskiya, rikon amana,  So da kaunar jama'a sune halayar Dan'Majen Gwandu


3- MENE NE AYUKKAN INJINIYA AHMED UMAR FAROUK (DAN MAJEN GWANDU) ?

Ba tare da dogon bayani ba; Bautan Allah, Alheri, Kyauta,  da Tausayin bayin Allah sune ayukkan da kowa ya shaidi Dan Majen Gwandu da su
____________________
Ahmed Umar 
Publisher Kebbi-Trust Online Newspaper 
ahmadugamji@gmail.com 
07038182929

Post a Comment

0 Comments