Kebbi-Trust Online Newspaper
*Cin Zarafin Jinsi: Akalla Masu Laifukan Cin Zarafi 50 Ne Aka Yankewa Hukunci Daga Watan Janairun 2024 Sakamakon Kafa Kotuna Biyu Na Musamman A Jahar Kebbi.*
Rahotanni sun bayyana cewa mutane fiye da 50 ne suka fuskanci hukunci wadanda ake zargi da laifukan cin zarafin jinsi daban daban da suka hada da fyade da sauransu.
Khadija yar kimanin shekaru 9 da haihuwa ta shiga wani yanayi bayan wani matashi mai shekaru 30 zuwa 40 da ake zargi mai suna Aliyu gidan kulu Mai Kosai da cin zarafinta ta hanyar yimata fyade.
“Ina cikin gida sai naji sallama Aliyu yana cewa a bada kunu, sai na fito na amso kudi, koda nazo mamata na bacci na bugeta taki tashi ina dauko kunu na azamata a kafa sai taji sanyi ta bude ido, Sai nabata kudi sai naje inbashi Kunun.” inji khadija.
“Sai yace in kawo mishi Kunun wurin dakin shi da yake gidan mu da gidan su babu nisa. Koda naje ban same shi cikin dakin ba ashe yana cikin bandaki dake kusa da dakin shi Ina fitowa sai ya ja hanuna ya shiga dani cikin bandakin ya cire min wando na ya fara lalata.”
Sai dai tuni hukumomi suka tsare shi tareda hukuntashi.
Wannan ba shine karon farko da aka taba samun nau’in cin zarafi ba, inda bayanai suka nuna cewa ko a watannin baya wata babbar kotu a wannan jaha, ta yankewa wani matashi mai suna Jamilu Abdullahi da ke kauyen Dan-Warai a Karamar Hukumar Aliero hukuncin daurin rai da rai kan yi wa wata yarinya ‘yar shekara takwas da haihuwa a duniya fyade wanda yarinyar kurma ce.
Hakama ko a karamar hukumar Argungu wata kotu ta yankewa wani matashi mai suna Badamasi Abdullahi mai shekaru 25 hukuncin daurin rai da rai bisa samunshi da laifin yiwa wata yarinya yar kimanin shekara 16 da haihuwa fyade.
Laifin fyade dai yana da hukunci a karkashin sashe na 210 na dokar Penal Code ta Jihar Kebbi na 2021.
Rahotanni daga ma’aikatar lamurran mata ta tarayya sun nuna cewa daga watan nuwamban shekarar 2023 ansamu laifukan cin zarafi akalla 27,698 a daukacin fadin kasa.
Mahaifiyar Khadija(ummi) yar kimanin shekara 9 da haihuwa wacce ta fuskanci cin zarafi na fyade, ta bayyana irin yanda lamari ya faru da yar ta, da kuma yanda ta jajirce wurin bayyana abinda ya faru domin a hukunta wanda yayi wannan aika aikar. Ta kuma jinjinawa cibiyar Mai Talle Tara SARC da irin gudumuwar da suka bada wurin ba khadija kulawa da kuma basu tai makon da ya dace .
A nashi bangaren sakataren hadaddiyar kungiyar dake yaqi da cin zarafin jinsi wato Technical working Group on GBV a jahar kebbi Comrade Nasir Idris yace matukar al’umma basu fitar da tsoro da fargaba ba sun fito suna bayani idan har wani abu ya samesu to babu shakka baza’a shawo kan matsalar cin zarafin jinsi ba.
“Alamarin cin zarafin jinsi yazama ruwan dare musamman ga qana nan yara mata da maza, Wannan kungiya, kungiya ce da akalla tayi hadaqa da kungiyoyi da yawa da sauran ma’aikatu da suka shafi cin zarafin jinsi.
“Domin taimakama al’umma, kuma kungiyar na shiga lungu da sako wajen yekuwa da wayarda kan jama’a gameda cin zarafin jinsi kuma idan ya faru akai kara kada a rufe domin hukunta wanda yayi laifi” Inji Nasir.
“A tarihi ba’a taba samun gwamnatin da ta nuna kulawa irin wannan ta Dr Nasir Idris Kauran Gwandu, musamman Uwar Gidanshi Hajiya Zainab Nasir Idris Kauran Gwandu wacce tayi tsayin daka domin ganin ankawar da wannan matsala ta cin zarafi. Tana bayarda naira 500,000 duk wata domin tallafawa wadanda aka ciwa zarafi”.
“Akwai kuma kudin zuwa da komawa da kudin magani kyauta da na abinci duk domin asamu sauki ga wannan matsala ta cin zarafin jinsi”.
“Babban kirana ga al’umma shine, muna rokon idan abu yafaru adaina sasantawa ko yin shiru a fito a bayyana domin hukuntawa, wanda hakan zaisa asamu saukin shawo kan matsalar” A cewar Nasir.
Da take tsokaci wakiliyar shugabar cibiyar dake fafutukar yaqi da cin zarafi da kuma tallafawa wadanda lamarin ya rutsa dasu mai suna Talle Tara Sexual Assault Referral Center dake garin Kalgo, Nurse Balkisu Bawa tace tun kafa cibiyar da gwamnatin jaha tayi ana tallafawa wadanda aka ciwa zarafi da duk wata gudumuwa da suke bukata, tareda tabatarda cewa anyi musu adalci akowane yanayi.
Balkisu Bawa ta kara da bayyana mana irin taimakon da suke ba wadanda aka ci zarafi su domin ingata rayuwar su.
“Muna bada taimakon gaggawa ga wadanda aka ciwa zarafi kowane iri kuma, haqiqa gwamnatin jaha nataka muhimmiyar rawa wajen ganin ansamarwa duk wanda yasamu kanshi cikin wani nau’in cin zarafi da ya kunshi, tallafi da zata ko zai tsayu da kafafunshi domin kore mishi damuwa ko rage radadin halin da yashiga” Inji Balkisu.
“An samar wa yanda aka ci zafarin su kayan sana’o’e daban daban da tallafin kudi wanda bazan iya lisafawa ba kasan cewar abin da yawa, munada sashe daban daban a cibiyar mu domin gwaji idan har wani abu yafaru, kuma a shirye muke mubi hakkin duk wanda aka ciwa zarafi wanda yazo cibiyar mu har sai mun tabbatar an hukunta wanda ya aikata laifin”.
“Daga Karshe ina son in shaida ma al’umma cewa wannan yaqi da cin zarafi da akeyi uwar gidan gwamnan jaha hajiya zainab nasir idris kauran gwandu itace ke jan ragamar wannan yaqi wanda akan haka muke da yaqinin cewa za’ayi nasarar wajen kawo karshen matsalar cin zarafi a wannan jaha kasancewar a yanzu babu sani ba sabo”.
Shima da yake bayani uban kasar marafa kuma Magajin Bunga Alhaji Idris Umar yace suna iya kokarin su wurin bin kadin duk Wanda aka ci zarafi, ya kuma yi kira ga al’umma dasu dena kyamatar wadanda ibtila’in cin zarafi ya sama. “Dolene a yabama kokarin gwamnatin jaha na kafa kotuna biyu domin yaqi da cin zarafin jinsi da kuma shirya taruka domin fadakar da al’umma game da illar cin zarafi. ina kira ga al’umma dasu bada goyon baya domin ganin kwalliya tabiya kudin sabulu” inji Magajin Bunga.
Masana dai na ganin cewa matsalar cin zarafin jinsi abune da yashafi kowa kuma dolene sai an hada karfi da karfe domin ganin an shawo kan matsalar.
Post a Comment
0 Comments