Kebbi-Trust Online Newspaper
KAMFANIN GINE-GINE; HA'AB ENGINEERING ZAIYI KAWANCE DA GIDAUNIYAR AISHA BELLO KA'OJE
Bisa la'akari da gudumuwar da taimakon da Gidauniyar AISHA BELLO KA'OJE CARES FOUNDATION ke bayarwa a dukkan fadin Jihar Kebbi, Kamfanin Gine-gine Mai suna HA'AB ENGINEERING NIG LTD ya kuduri yin aiki tare da wannan Gidauniyar domin tallafawa al'umma maza da mata.
A lokacin da yake ganawa da shugaban Gidauniyar, Shugaban Kamfanin HA'AB ENGINEERING, Injiniya Habibu Usman Geza yace yayi matukar gamsuwa da ayukkan alheri da Gidauniyar AISHA BELLO KA'OJE CARES FOUNDATION take aiwatar wa a Jahar Kebbi, don haka ya Yanke shawaran aiki tare domin bayar da gudumuwar sa domin ci gaba da aiwatar da ayukkan wannan Gidauniyar.
Injiniya Habibu yace bada jimawa ba, zai dauki nauyin wasu aikace-aikacen wannan Gidauniyar domin tallafawa al'umma maza da mata a Jahar Kebbi.
Da yake jawabi, Shugaban Gidauniyar, Kwamared Abubakar Abdulkadir ya nuna farin cikin sa da Jin dadin sa bisa wannan kuduri na Kamfanin HA'AB ENGINEERING
Kwamared Abubakar Abdulkadir yayi kira ga sauran masu hannu da shuni a Jahar Kebbi da suyi koyi da Kamfanin HA'AB ENGINEERING NIGERIA LIMITED wajen yin kawance da kungiyoyi masu zaman kansu domin taimakawa wa al'umma musanman marayi, mata da matasa.
Post a Comment
0 Comments