ALLAH YA KARAWA KAURA NASARA!
SANARWAR TAYA MURNA GA MAI GIRMA GWAMNA:
Ni, Hon. Nura Bala Fingillah Kwamishinan kula da harkokin Matasa da wasanni na Jihar Kebbi Ina amfani da wannan dama domin taya Mai girma Gwamnan Jihar Kebbi, Alh.Dr. Nasir Idris (Kauran Gwandu) da al'ummar Jihar Kebbi Baki daya murnar nasarar da muka samu a Kotun Koli.
Wannan nasara ce ba wai ga Mai girma Gwamna kadai Ba har da al'ummar Jihar Kebbi Baki daya, domin wannan nasara zata bamu dama mu cigaba da ayyukan alkhairi da Mai girma Gwamna ya Fara aiwatarwa al'ummar Jihar Kebbi.
Muna kuma rokon al'umma Ku cigaba da baiwa Gwamnati mai ci a Jihar Kebbi, karkashin Mai daraja Gwamna Nasir Idris Kauran Gwandu hadin Kai da goyon baya domin mu Kai ga samun nasarar aiwatar da ayyukan raya kasa da Kawo cigaban al'umma dana jihar Kebbi Baki daya.
Allah ya ja zamanin Mai girma gwamna da Jihar Kebbi da Nigeria Baki daya.
Nagode
Hon. Nura Bala Fingillah Kwamishinan kula da harkokin Matasa da wasanni na Jihar Kebbi
Post a Comment
0 Comments