MALAMI YA KARYA FARASHIN KAYAN ABINCI A JIHAR KEBBI

ABUBAKAR MALAMI, SAN YA SAUKARDA FARASHIN KAYAN ABINCI A KASUWA

Dahiru Baiti, Ahmad Umar

 Bayanai daga kasuwannin kayan abinci dake fadin jahar Kebbi na nuna  cewa farashin Shinkafa ya kare yayi kasa sosai  dalilin aikin alkhairi na rabon shikafa da maigirma Ministan Shari'a na Nijeriya yayi a fadin jihar kebbi.

Kafin raba wayannan kayan abinci da Malami ya yi, ana sayen mudun  shinkafa akan ₦700 amma yanzu cikin ikon Allah farashi yayi kasa zuwa ₦520. Haka labarin yake a farashin gero inda nan ma farashin ya sauka.

Abubakar Malami, SAN bai tsaya anan ba harda Suga  ya rabawa  al'umman jihar Kebbi.

 Magidanta da dama ne suka fita zullumi akan abincin azumi sanadiyar wannan ruwan abinci da Abubakar Malami ya yi.

Da fatar wayanda suka samu fiye da kima zasu ji tsoron Allah su yanma makwabtan su domin samun ladan Ubangiji Allah.

Muna rokon Allah Ya kara sanya wa dukiyar Abubakar Malami albarka, ALLAH YA BIYA MASA DUKKAN BUKATUN SA NA DUNIYA DA LAHIRA, AMIN.

Post a Comment

0 Comments