YANZU-YANZU

YANZU- YANZU:

KOTU TAYI FATALI DA KARAR YAN APC MASU JAYAYYA A JIHAR KEBBI

A yau Alhamis 17-03-2022, babbar kotun tarayya dake Birnin kebbi tayi watsi da kararrakin da wasu suka kai gabanta domin kalubalantar zababbun Shugabannin jam'iyar APC karkashin jagorancin Abubakar Kana Zuru.

Idan za a tuna bayan kammala zaben Shugabannin APC a matakin jaha da kananan hukumomi sai kwatsam bangaren tsohon shugaban jam'iya Hon. Bala Kangiwa suka kai kara suna neman kotu ta soke zabukkan da akayi na Shugabannin APC a fadin jahar Kebbi baki daya.

Kotun tayi watsi da kararrakin ne saboda rashin gamsassun hujjoji daga bangaren masu shigar da karar.

A kwanakin baya a wani sako na murya da ya bayyana a kafafen yada labarai na zamani anji jagoran wannan bangaren na masu kara, Sanata Adamu Aleiro na cewa idan kotu bata basu gaskiya ba, za su bar jam'iyar APC. Sanata Aleiro na kan bakansa akan wannan barazanar ko ya canza shawara?. Lokaci zai nuna.

Post a Comment

0 Comments