TARON APC A ABUJA: Malami Yayi Abin Mamaki

TARON APC A ABUJA: Malami Yayi Abin Mamaki

www.kebbitrust.com

Ministan Shari'a na Nijeriya, Abubakar Malami ya nuna bajinta a taron APC a Abuja, inda ya tanadar wa tawagar jahar Kebbi waddacen abincin da akaci aka bari.

Majiyar Kebbitrust ta tabbatar da cewa daruruwan mutane ne Abubakar Malami ya gayyata daga jahar Kebbi tare da tanadar masu wadataccen abinci da abin sha.

Majiyar ta nuna dukkan wanda bai sami muhalli ba ambashi wadatattun kudade na kama daki a hotel, amma abinka da malam Bahaushe maimakon zuwa hotel sai wasu suka share titi kawai sukayi kwancin su, suka soke kudaden su a aljihu.

Wasu da su san abinda ya faru ba, sai suka dinga daukar hoton mutanen suna cewa an kawo su Abuja an yi watsi da su, domin cinma wani buri na siyasa.

Game da abinci kuma, maimakon kowa ya dauki leda daya na 'take-away' sai kaga mutun ya dauki leda 4 ko fiye, amma duk da haka sai da kowa ya gudu ya bar abinci ana neman wayanda za'a ba ba'a samu ba.

Cikin taimakon Allah dukkan daruruwan mutanen da suka karbi gayyatar Abubakar Malami sunje Abuja lafiya sun dawo gida Kebbi lafiya.

Post a Comment

0 Comments