SEN. ALEIRO YA ZIYARCI MALAMI A ABUJA

SEN. ALEIRO YA ZIYARCI MALAMI A ABUJA

Daga: Ahmad Umar

Rahotanni daga Abuja na nuna saura kiris a dinki  sabanin siyasar Jahar Kebbi. 

A ziyarar ba zata da Sanata Adamu Aleiro ya kaiwa Ministan Shari'a Abubakar Malami na nuna cewa an Sami fahintar juna a tsakanin wayannan jigogin siyasar Jahar Kebbi.

Idan za a tuna a satin da ya gabata Gwabna Mai ci Atiku Bagudu shima  yakai irin wannan ziyarar bazata a gidan Yayansa Sanata Adamu Aleiro a Birnin Kebbi.

A kwanakin baya ma anji jigo a bangaren Adamu Aleiro watau Alhaji Sani Dododo na fada a wata tattaunawa da gidan Radio Equity FM, cewa da zarar Gwamna Atiku Bagudu da Minista Abubakar Malami da Sanata Aleiro sun fahinci junan su shikenan matsalar APC a jahar Kebbi ya zama tarihi.

Ana kyautata wayannan ziyarce ziyarcen ba zata zasu haifar da da mai ido InshaAllahu.

Post a Comment

0 Comments