Takarar Sanata Aleiro a 2027: BA A GAJIYA DA ALHERI
Takarar Sanata Aleiro a 2027: BA A GAJIYA DA ALHERI
KEBBI TA TSAKIYA 2027: SANATA ALEIRO ALHERI NE, BA A GAJIYA DA ALHERI: Shawara zuwaga Kabiru Giant
Daga: Ahmed Umar
Nayi matukar mamaki da naji cewa Kabiru Sani Giant ya bijirewa alfarmar da shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya nema ta hannun mai girma Gwamna,Dr. Nasir Idris, akan takarar Sanata Adamu Aleiro a 2027.
Da farko nayiwa Kabiru Giant uzuri, cewa kila yanada babban dalilin wannan fajirci na siyasa, amma da karshe sai na fahinci babban dalilin sa shine Wai 'AN GAJI DA BABA ALEIRO'; Ban San wanda ya gayawa Kabiru Giant cewa ana GAJIYA DA ALHERI ba.
DALILIN DANGANTA SIYASAR SANATA ALEIRO DA ALHERI
Zan takaita ayukkan alheri da Sanata Aleiro ya aiwatar a jahar Kebbi da suke binsa har yanzu:
- Sanata Aleiro lokacin da yayi Gwamna jahar Kebbi, ya sakarwa kananan hukumomi kudaden su; Aleiro ya kafa TENDER BOARD domin bayar da kwangila ga kowa da kowa, mai galihu da marar galihu; Aleiro yaba Commissioners damar daukar ma'aikata da sauransu. Wannan yasa Arziki ya watsu a Jihar Kebbi da kuma ba Aleiro damar jan zaren sa har yanzu. (Cikin Gwamnonin da suka biyo bayan Aleiro akwai wanda ya rike kudaden Kananan hukumomi; Ya kashe TENDER BOARD, daga shi sai P. A dinsa kawai keyin kwangila, ba Commissioner ko daya dake iya daukar ko messenger aiki a gwamnatin sa, TALAUCI ya mamayi Jihar Kebbi Sakamakon wannan son kai, shi yasa zaren wannan Gwamna ya tsinke tun yana bisa mulki, domin yayi takara ya kama kasa)
- Aleiro ya samar wa garuruwa da kauyukka sama da 100 wutar lantarki da hanyoyi- Sakamakon haka mutane da dama sun samu sana'o'in yi
- Aleiro ya gina Jami'a (University) da School of Nursing, nanma daruruwan mutane sun samu ayukkan yi
- Cikin kananan hukumomi 21 dake jahar Kebbi ba karamar hukumar da Aleiro bai dibi mutane ya basu kwangiloli ba- wannan ne sirrin da yasa Aleiro ya zama IKON ALLAH SAI KALLO a siyasar jahar Kebbi.
- Aleiro ya taimakawa karatun dubban ya'yan talakawa, ni kaina AHMED UMAR, Aleiro ne ya saya mini JAMB FORM da na shiga Jami'a (BUK)- Sanadiyar wannan karatun, na sami rufin asiri gwargwado, Na godewa ALLAH, na kuma godewa Baba Adamu Aleiro.
- Sanata Aleiro ne ya fara gina filin jirgin sama na jahar Kebbi (Sir Ahmadu Bello International Airport Birnin Kebbi) nan ma dubban mutane ne ke anfana da shi.
Wayannan kadan ne daga ayukkan alheri da Sanata Aleiro ya aiwatar a Jihar Kebbi dake binsa har yanzu. DON HAKA, ALEIRO ALHERI NE, KUMA BA A GAJIYA DA ALHERI.
ANA BARIN HALAS KO DON KUNYA
Ayau Kabiru Giant bayada manyan masoya ko masu gida a siyasar jahar Kebbi irin mutune biyu: Mai Girma Gwamna jahar Kebbi Dr. Nasir Idris Kauran Gwandu da kuma Dan Gwamna: Injiniya Ahmed Umar Farouk (Danmajen Gwandu) MD, NAMA mai TKG.
Kabiru Giant na sane cewa wayannan bayin Allah sun taimaka masa, sannan kuma sunada alfarma a wurin sa. Sunyi wa shugaban kasa alkawalin isar da sako, sun isar - komai HALALLACIN da Kabiru Giant ke dashi ya kamata yayi hakuri da wannan takarar domin KUNYAR KAURAN GWANDU da DANMAJEN GWANDU.
Kabiru Giant yayi hattara da jifar gafiyar Baidu; ba wan ba wan 'MARUS'. Kada a rabashi da Kaura da Danmaje da Karshe kuma ayi watsi da shi. Don anyiwa wayanda suka fishi wayo haka.
ALLAH YABA BABBAN YAYA, KABIRU GIANT IKON BIYAYYA GA SHUGABAN KASA DA GWAMNAN JIHAR KEBBI, DR. NASIR IDRIS KAURAN GWANDU- Idan kuma yana ganin wancan shine masoyin sa ba Kauran Gwandu ba; Toh aji dadi lafiya.

Post a Comment
0 Comments