Tarihin Dan'majen Gwandu (Kashi Na 11)
ASAN MUTUM; ASAN HALIN SA; ASAN AIKIN SA :SHARHI AKAN RAYUWAR DAN'MAJEN GWANDU*
( Kashi Na 11)
KADAN DAGA CIKIN AYUKKAN ALHERIN DAN'MAJEN GWANDU A JAHAR KEBBI
Sanin mutum da sanin halin sa da kuma sanin aiki sa, sune ma'aunin hankali da mutane ya kamata suyi la'akari da su wajen ma'amala ta yaro da uban-gida da kuma wajen zaben shugabanni.
A wannan kashi na 11, akan sharhin tarihin Injiniya Ahmad Umar Farouk (Dan Majen Gwandu, Gamjin Kabi) Kuma Shugaban Hukumar Kula da Sararin Samaniya na Nijeriya (watau MD, Nigeria Airspace Management Agency 'NAMA') zamuyi takaitaccen bayani akan kadan daga cikin ayukkan alherin da ya aiwatar a jihar Kebbi a matsayin sa na MD, NAMA.
1-WANE NE INJINIYA AHMED UMAR FAROUK (DAN MAJEN GWANDU)? kashi na 11:
Wasu mutane da dama sun rike manyan mukamai a matakin Gwamnatin tarayya, amma ko yan'uwan su basu taimakawa ba, balantana mutanen jiha baki daya.
Alhamdulillah, Dan'majen Gwandu ya sami dama kuma ya'yi anfani da damar yadda ya dace ta hanyar kawo ci gaba da taimakon mutanen jihar Kebbi kamar haka:
1- INGANTA FILIN JIRGIN SAMA NA JAHAR KEBBI
A matsayin sa na shugaban hukumar kula da sararin samaniya ta Nigeria (watau MD Nigerian Airspace Management Agency NAMA ) Dan'majen Gwandu ya Samar da na'urorin zamani da suka mayar da filin sauka da tashin jiragen sama na jihar Kebbi, (watau Sir Ahmadu Bello International Airport, Birnin Kebbi) daya daga filayen jiragen sama mafi inganci a Nijeriya.
Dan'majen ya samar da mafi akasarin dukkan na'urorin da ake bukata a filin jirgin sama: Mutanen Kebbi Sun Gode
2-DAUKAR MATASA AIKI
Dan'majen Gwandu yayi anfani da wannan damar da Allah Ya bashi, Ya dauki ya'yan talakawa da dama aiki a hukumar sa ta NAMA da ma wasu ma'aikatun Gwamnatin tarayya.
Tun Yan 'social media' na lissafin yawan matasan da ya dauka aiki har lissafin ya bace masu saboda Dan'majen Gwandu bai bayyana mutanen da ya dauka aiki, sai dai su bayyana kan su; A nan ma mutanen jihar Kebbi sun gode
3- KYAUTAR AZO A GANI
Kamar yadda na fada a kashi na 1, Allah Ya albarkaci Dan'majen Gwandu da sakakken hannu kamar yadda Hausawa ke cewa.
Dan'majen Gwandu yayi kama da dan'uwansa Marigayi Sir. Ahmadu Bello (Sardaunan Sokoto) da kuma surikin sa, His Excellency Dr. Nasir Idris (Kauran Gwandu) wajen kyauta.
Idan Dan'majen Gwandu yayi ma kyauta, ko ance kadawo gobe ba zaka dawo ba don kunya. A nan ma mutanen jihar Kebbi sun gode.
4- GIDAUNIYAR DAN'MAJEN GWANDU
Dan'majen Gwandu ya taimaki jama'a Maza da mata, musanman marasa lafiya ta hannun Gidauniyar sa mai suna Dan'majen Gwandu Foundation
5- GUDUMUWA GA JAM'IYAR APC
a- Dan'majen Gwandu ya kirkiro da kungiyar TKG da ke fatar zarcewan Shugaba Tinubu da Gwamna Nasir Idris; a tarihin siyasar Kebbi ba a taba kungiya da mutun daya ya kafa tayi tasiri da cikakkun kayan aiki irin TKG; mutanen jihar Kebbi da Shugaba Tinubu da Gwamna jihar Kebbi Dr. Nasir Idris sun gode
b- Dan'majen Gwandu ya bayar da kyauta mafi tsoka ta Naira miliyan 100 (N100m) ga sabuwar kungiyar Tinubu/Kauran Gwandu 2 times.
c- Dan'majen Gwandu ya bayar da kyauta mafi tsoka ta sama da Naira miliyan 50 (N50m) ga gidauniyar maman sa, Uwargidan Gwamna jihar Kebbi (watau NASARA FOUNDATION)
d- Dan'majen Gwandu ya raba raguna 100 ga shugabanin jam'iyar APC a lokacin bikin babban sallar da ta gabata
e- Dan'majen Gwandu yayi ruwan kudi ga sauran jama'ar jihar Kebbi kafin bikin sallah da bayan bikin sallah da sauran su.
Mu hadu a kashi na 12:
A kashi na gaba watau Kashi na 12 na kuma karshe a wannan sharhi na tarihin Dan'majen Gwandu, zamu yi bayani akan ra'ayin jama'a akan halayan Dan'majen Gwandu In Sha Allah.
2- MENE NE HALAYAN INJINIYA AHMED UMAR FAROUK (DAN MAJEN GWANDU)?
Gaskiya, rikon amana da so da kaunar jama'a sune halayar Dan'Majen Gwandu
3- MENE NE AYUKKAN INJINIYA AHMED UMAR FAROUK (DAN MAJEN GWANDU) ?
Bautan Allah, Alheri, Kyauta, da Tausayin bayin Allah sune ayukkan Dan Majen Gwandu
____________________
Ahmed Umar
ahmadugamji@gmail.com
07038182929
Post a Comment
0 Comments