Tarihin Dan'Majen Gwandu (Kashi Na 7)

ASAN MUTUM; ASAN HALIN SA; ASAN AIKIN SA : SHARHI AKAN RAYUWAR DAN'MAJEN GWANDU

           ( Kashi Na 7)

 Dan'Majen Gwandu A Hukumar NAMA 

Daga Ahmed Umar 
Sanin mutum da sanin halin sa da kuma sanin aiki sa, sune ma'aunin hankali da mutane ya kamata suyi la'akari da su wajen ma'amala ta yaro da uban-gida da  kuma wajen zaben shugabanni.

A wannan kashi na 7, akan sharhin tarihin Injiniya Ahmad Umar Farouk (Dan Majen Gwandu, Gamjin Kabi) Kuma Shugaban Hukumar Kula da Sararin Samaniya na Nijeriya (watau MD, Nigeria Airspace Management Agency 'NAMA') zamuyi takaitaccen bayani akan aikace-aikacen sa a hukumar kula da sararin samaniya ta Nijeriya (watau Nigeria Airspace Management Agency 'NAMA')





1-WANE NE INJINIYA AHMED UMAR FAROUK (DAN MAJEN GWANDU)? kashi na 7:


Injiniya Ahmad Umar Farouk (Dan'Majen Gwandu) ya fara aiki a hukumar kula da sararin samaniya ta Nigeria  (watau Nigeria Airspace Management Agency 'NAMA') a shekarar 2002 bayan ya baro Ma'aikatar kwadago ta Gwamnatin tarayya
Dan'Majen Gwandu yayi aikace aikace da kuma rike mukamai da dama a wannan babban hukumar mai kula da sararin samaniya ta Nijeriya (Nigeria Airspace Management Agency 'NAMA') kamar haka:

- Dan'Majen Gwandu ya fara aiki a NAMA a matsayin babban Injiniya a filin jiragen sama da ke Abuja (Watau Chief Engineer Abuja Airport) a tsakanin shekaran 2002 zuwa 2006.

- Dan'Majen Gwandu ya sami karin girma zuwa babban manaja mai kula da sararin samaniya na filin jiragen sama dake Minna Jahar Niger (Airspace Manager, Minna Airport) tsakanin shekara 2006 zuwa 2009

- Dan'Majen Gwandu ya kara samun daukaka zuwa babban manaja mai kula da bayarda kwangila da kashe kudin hukumar NAMA (General Manager Procurement) tsakanin shekara 2009 zuwa 2012

- Dan'Majen Gwandu ya rike mukamin babban manaja na musanman mai kula da yankin Arewacin Nijeriya baki daya (General Manager Special Projects 'NORTH') 2012 zuwa 2016

- Dan'Majen Gwandu ya kara samun karin girma zuwa Darakta mai kula da dukkan na'urorin filayen jiragen sama da ke Nijeriya (watau Director Safety Electronic and Engineering Services 'DSEES')  a shekaran 2016 zuwa 2023.

ALLAH YA MALLAKARWA DAN'MAJEN GWANDU HUKUMAR NAMA BAKI DAYA:
Cikin iyawar Sa da Kudiran Sa a shekara ta 2023 Allah Ya Daukaka Dan'Majen Gwandu zuwa matsayin da hausawa ke kira 'Oga kwata -kwata' a hukumar NAMA; (Watau 'Managing Director -MD') wanda shine kololuwan kujera a hukumar NAMA.
Muna rokon Allah Ya tayashi riko, Ya bashi nasaran aiwatar da dukkan ayukkan alherin da ya tsara aiwatarwa.

NASARORIN DAN'MAJEN GWANDU A HUKUMAR 'NAMA' A MATSAYIN SA NA 'MD'...........

 Mu hadu a kashi na 8  : A kashi na gaba watau Kashi na 8, zamuyi karin bayani akan nasarori da ayukkan alherin da Dan'Majen Gwandu ya aiwatar, yake kuma kan aiwatarwa a wannan hukuma ta NAMA In Sha Allah 



2- MENE NE HALAYAN INJINIYA AHMED UMAR FAROUK (DAN MAJEN GWANDU)? 

 Gaskiya, rikon amana da so da kaunar jama'a sune halayar Dan'Majen Gwandu


3- MENE NE AYUKKAN INJINIYA AHMED UMAR FAROUK (DAN MAJEN GWANDU) ?

 Bautan Allah, Alheri, Kyauta,  da Tausayin bayin Allah sune ayukkan Dan Majen Gwandu

____________________
Ahmed Umar 
ahmadugamji@gmail.com 
07038182929

Post a Comment

0 Comments