Shugaban Matasan Arewa Yayi Ta'aziya

Harin Yan Ta'adda A Augie: SHUGABAN KUNGIYAR TAFIYAR MATASAN AREWA NA YANKIN AREWACIN NAJERIYA: Muhammad Sanusi Zazzagawa 
da Shugaban Kugiyar Na jahar Kebbi Engr. Abubakar Isah Albani Yauri Sunyi wa Gwamnan Jahar Kebbi Ta'aziya
Shugaban kungiyar Tafiyar Matasan Arewacin Nijeriya,Muhammad Sanusi Zazzagawa da shugaban kugiyar na jahar Kebbi Engr. Abubakar Isah Albani Yauri Sunyi wa Gwamnan Jahar Kebbi Dr. Nasir Idris (Kauran Gwandu) ta'aziyar harin da yan ta'addan Lakurawa suka kai a Yola 'Ward' dake cikin karamar hukumar mulki ta Augie da ke masarautar Argungu dake Jahar Kebbi.
Har ila yau shugabannin sun mika irin wannan ta'aziyar ga mai Martaba Sarkin Kabin Argungu Dr. Sama'ila Muhammad Mera (CON)da yan Majalissar sa Hon. Sani Yakubu Yar Giwa Dan Majalissar Tarayya Mai Wakiltar Argungu Augie,
Da Uban Kasar Augie.

Da yake mika ta'aziyar Sanusi Zazzagawa ya kara da kira ga Maigirma Gwamna Dr. Nasir Idris Kauran Gwandu da yakara azama domin ganin an kawo karshen wannan ta'addanci a fadin Jahar Kebbi musanman a kananan hukumomin Augie, Arewa da Dandi

Da karshe Sanusi Zazzagawa yayi addu'a Allah Ya taimaki Masarautar Argungu Da Gwamnatin Jihar Kebbi Ya kawo  karshen wayannan matsaloli.

Zazzagawa ya kuma roki Allah da ya kawo karshen duk wani azzalumi shugaba ko mabiyi dake da hannun wajen wannan kisan gilla da ke faruwa a Nijeriya. 
_____________________
 Daga: National Auditor General Comrade Yakubu Abubakar Kamba

 For: Tafiyar Matasan Arewa RESHEN JAHAR KEBBI

Post a Comment

0 Comments