Kebbi-Trust Online Newspaper
An gudanar da bikin yaye ɗalibai 64 waɗanda maigirma sakataren Gwamnatin Jihar Kebbi Alhaji Yakubu Bala (Tafidan Yawuri) ya ɗauki nauyin koya musu sana'ar ɗinki:
Daga Sani Twoeffect Yawuri
An gudanar bikin yaye ɗaliban ne ranar asabar 26/4/2025 a cikin garin Yawuri inda Maigirma sakataren Gwamnatin Jihar Kebbi ya samu halartar bikin.
Maigirma Tafidan Yawuri ne ya ɗauki nauyin koyar da ɗaliban maza da mata ɗinki a matsayin wata hanya ta taimakawa matasa domin samun sana'o'in dogaro dakai.
A yayin bikin yaye ɗaliban, Maigirma sakataren Gwamnatin ya baiwa ɗaliban rukuni na farko su 30 kekunan ɗinki domin fara gudanar da ɗinkin kamar yadda suka koya inda su kuma kaso na biyu mutum 34 za'a basu nasu kekunan ɗinkin daga baya.
A wurin taron yaye ɗaliban, haɗaɗɗiyar kungiyar teloli ta Yawuri a ƙarƙashin jagorancin shugabanta Rilwanu Sani Sani Rilwanu ta karrama sakataren Gwamnatin a matsayin gwarzon siyasa da son cigaban matasa ƙasar Yawuri.
Haka kuma bikin ya samu halartar manyan baƙi daga ciki da wajen masarautar Yawuri da suka haɗa da: Alhaji Abubakar Sadiq Yelwa (Katukan Yawuri), Alhaji A.I Suru, Honorabul Bala Muhammad Bala Gagga, shugaban ƙaramar hukumar mulki ta Yawuri Honorabul Abubakar Shuaibu (Ƙauran Yawuri), shugaban ƙaramar hukumar mulki ta Ngaski Honorabul Maniru Abubakar Warah, Shugaban jam'iyyar APC na garin Yawuri Alhaji Yusuf Alhassan, Alhaji Zaki Mental, Alhaji Abdullahi Mai Akwai daidai sauransu.
Haka kuma a wurin bikin manyan baki daban-daban sun bayar da gudunmawa daban-daban ga kungiyar teloli da kuma ɗaliban da aka yaye.
1. Alhaji Abubakar Sadiq Yelwa (Katukan Yawuri) ya bayar da gudunmawar ₦500,000 ga kungiyar domin kara inganta ayyukan ta.
2. Alhaji A.I. Suru ya bayar da tallafin kuɗi ₦20,000 ga kowani ɗalibi da aka yaye .
3. Honorabul Bala Muhammad Gagga ya bayar da gudunmawar ₦100,000 ga kungiyar domin inganta ayyukan ta da dai sauran kyaututtuka daban-daban.
Post a Comment
0 Comments