2027: Jahar Kebbi Sai Kauran Gwandu
2027: Jahar Kebbi Ta Kaura Ce In Sha Allah ___Inji Dan'Majen Gwandu
Shugaban mashahuriyar kungiyar 'Tinubu Kauran Gwandu Continuity' (TKG) kuma shugaban Hukumar kula da sararin samaniya ta Nijeriya (watau MD, Nigeria Airspace Management Agency 'NAMA') Injiniya Ahmad Umar Farouk (Dan'Majen Gwandu) ya ayyana cewa babu gurbi a kujeran Shugaban kasa da ta Gwamnan jihar Kebbi a zaben 2027 mai zuwa.
Dan'Majen Gwandu ya shawarci duk wani mai shawan hawa kujeran Shugaban kasa da ta Gwamnan jihar Kebbi da suyi hakuri har zuwa 2031 bayan kammala mulki na biyu na shugaba Tinubu da Gwamna Nasir Idris (Kauran Gwandu).
Dan'Majen Gwandu yace ba wani kawance, zagon kasa da jita-jita da munafinci da zasu hana Kauran Gwandu zarcewa a Karo na biyu da yardan Allah.
Don haka sai ya umurci yan' hamanya da suyi hakuri su shigo ayi tafiya da su domin gina Sabuwar Nijeriya da Sabuwar Jahar Kebbi.
Post a Comment
0 Comments