Kebbi Trust Online Newspaper

ZANGA-ZANGA: Rundunar Ya Sandar Jihar Kebbi Ta Sanar Da Jibge Jami'an tsaro sama da 5,000 Domin Tabbatar Da Zaman Lafiya A Jiha

Rundunar Ya Sandar Jihar Kebbi Ta Sanar Da Jibge Jami'an tsaro sama da 5,000 Domin Tabbatar Da Zaman Lafiya A Jiha
Da yake zantawa da manema labarai, kwamishinan yan sandan jahar kebbi CP Bello Sani ya bayyana muhimmancin dake akawai na samar da Jami'an domin ganin an kare rayuwar Alumma.
Ya kuma bayyana cewa kundin tsarin mulkin kasar ya bayar da dama ga yan kasar dasu gudanar da zanga zangar lumana, amma kuma anja hankalin masu zanga zangar da kada su aikata wani abu da ka iya hddasa husuma a yayin zanga zangar.
kwamishinan hakam yakara dacewa shugabannin hukumomin tsaro a wannan jaha sunyi kira ga jagororin zanga zanga da su bayarda bayanan wuraren da zasu gudanar da zagaya, sunayen jagororinsu da kuma lokacin da zasu dauka suna gudanarda zanga zanga domin Samar masu da tsaro da kuma samun dammar kama masu kokarin fakewa da zanga zangar don cimma muradunsu.

Akan haka ya shawarci iyaye dasu kula da yaransu tareda shawartar alummar jaha d asu cigaba da gudanarda alamurransu na yau da kullum kada su ji tsoro ganin Jami'an tsaro  kasancewar zasuyi aikinsu ne na kare rayukan alumma da kuma samarda doka da oda afadin jaha.
A wani labarin kuma rundunar ta gabatarda naira miliyan 5  ga iyalai ukku na rundunar wadanda suka rasa rayukansu yayin da suke bakin aiki.
Iyalan sun godewa kwamishinan akan wannan kokarin tareda adduar Allah ma daukakin sarki da yacigaba da taimakon rundunar Yan sanda da Jami'an ta baki daya.

Post a Comment

0 Comments