Shugabanci Bisa Ra'ayin Jama'a A Dandi
SHUGABAN KARAMAR HUKUMAR DANDI DR. MANSUR ISAH NACI GABA DA SAURAREN AYUKKAN DA JAMA'AR DANDI KE BUKATA DAGA GWAMNATI
Sabanin yadda ake gudanar da mulkin jama'a a baya inda haka Kawai shugaban Karamar hukuma zai yanke shawaran aikin da zaiyiwa jama'a ba tare da yaji shawaran su ba, kuma ko suna da ra'ayi akan aiki ko basu da ra'ayi.
Kaucewa wannan tsohon tsarin ne yasa Shugaban Karamar Hukumar Dandi, Dr. Mansur Isah ya kirkiro da wannan sabon tsari na sa jama'a gaba su fadi irin ayukkan da suke so domin ci gaban su.
Yanzu dai an kammala sauraren ra'ayoyin jama'ar wards 9 da suka hada da Gezah, Shiko, Dolekaina, Maigwaza, Fana, Kyangakwai, Kwakkwaba, Banizumbu da Buma.
Kuma Dukkanin wayannan mazabun sunyi cikakken bayani akan irin ayukkan da suke so, sun Kuma bayar da su a rubuce domin aiwatar wa.
Dr. Mansur yayi alkawalin aiwatar da ayyukan dake karkashin karamar hukuma. Ayukkan dake karkashin jaha da Gwamnatin Tarayya Kuma Yayi alkawalin gabatar da su ga muhukunta da ke da alhakin aiwatar da su.
Ranar Attanin za a ji ra'ayin mazabun Kamba-Kamba da Maihausawa.
Bayan wannan za a fitar da cikakken rahoto da kuma labari akan manufofin wannan sabon tsari da Dr. Mansur Isah Kamba ya kirkiro.
Post a Comment
0 Comments