Shirin Shuka Itatuwa Miliyan Daya A Kebbi

*KUNGIYAR MATASA SUN KUDURI SHUKA ITACE MILIYAN DAYA A JAHAR KEBBI* 


Wasu fitattun Kungiyoyin matasa a Jahar Kebbi sun kuduri shuka itatuwa masu dinbim yawa a dukkan kananan hukumomi 21 dake fadin Jihar Kebbi.
Jagoran wannan tafiyar da akasawa suna a harshen turanci 'Tree Initiative for Environmental Sustainability (TIES), Alhaji Abubakar Naamare (Majikiran Jega)  ya bayyana cewa sun kuduri shuka itatuwa har miliyan daya a wannan shekara ta 2024 ta hanyar kawance da wasu kungiyoyi da jakadun  matasa da kuma wasu kungiyoyi masu zaman kansu domin tallafawa Gwamnatotin Tarayya da na Jahohi da na Kananan Hukumomi wajen kawar da barazanar canjin yanayi da ake fuskanta a duniya.
Naamare ya yabawa da goyon bayan da suka samu daga Kwamitin Kawancen akan canjin yanayi na Jihar Kebbi (Kebbi Development Forum's Committee on Environment and Climate Change) inda ya bayyana kwamitin a matsayin gimshiki wajen samun nasaran aikin da aka sa gaba.

Naamare ya yi kira ga daidaikun jama'a da kungiyoyin gwamnati da masu zaman kansu da su baiwa wannan yunkuri hadin Kai da gudumuwa ta hanyar shiga a dama da su wajen yekuwan shuka itatuwa ta hanyar anfani da hannayen su da kuma sa ido domin samun nasaran wannan kudurin.
Jagoran ya bayyana cewa matasa sune keda kaso 70 na yawan al'umma Jihar Kebbi da aka kiyasta sun kai miliyan 3 daga cikin al'umma kusan miliyan 5 da rabi da ake hasashen Jihar Kebbi ta mallaka; idan kowane matashi zai shuka icce daya ya kula da shi har ya girma, labari zai sha bamban nan da yan shekaru.

Don haka aka kirkiro da yekuwa da akasawa suna a harshen turanci OPERATION PLANT ONE MILLION TREES; ONE YOUTH-ONE TREE' da suka hada da kawancen matasa, dalibai, Kungiyoyin mata da sauran su duk an tanade su kuma za a bayyana su a bainar jama'a bada jimawaba. 
Ya kara da cewa ma'aikatar muhalli ta jiha da sauran masu ruwa da tsaki a fannin kare muhalli sune za asa gaba domin samun nasaran wannan kudurin.

A halin da ake ciki yanzu an sami gudumuwar sama da irran itace 2,000 daga jama'a, kuma ana nan anaci gaba da alkawalin bayarda gudumuwar itacen kafin kaddamar da shirin a hukumance.
 Bisa wannan ne ake kiraga ga al'umma da kungiyoyi dake da shawar bayarda gudumuwar itacen ko kayan kulawa da itacen da su tumtubi jagoran shirin na jaha; Alhaji Abubakar Naamare Majikiran Jega don yin kawance domin samun nasaran wannan kudurin na shuka itatuwa miliyan daya a Jahar Kebbi a cikin wannan shekaran na 2024.

Post a Comment

0 Comments