Ayukkan Alherin 'AGILE' A Jihar Kebbi
AYUKKAN ALHERIN DA SHIRIN 'AGILE-PROJECT' KE AIWATARWA A SASHEN ILMI A JAHAR KEBBI
Babi Na 1
Ahmad Umar
(Barkasa Communications)
Gwamnatin tarayyar Najeriya da na jihohi da kananan hukumomi da kungiyoyin tallafi na duniya, irin su Bankin Duniya (World Bank) da ita kanta majalisan dinkin duniya (United Nations) a can baya sun sha kirkiro da tsare- tsare (Project) da shirye shirye (programmes) domin shawo matsalar ilmi musanman a tsakanin yara mata, amma har yanzu da sauran rina a kaba.
Amma ga dukkan alamu ana iya cewa an samo bakin zaren walwale wannan matsalar ilmi a tsakanin yara mata ta hanyar kirkiro da wannan shirin na AGILE.
MENENE MA'ANAR SHIRIN AGILE?
Cikakken sunan shirin da harshen turanci shine; Adolescence Girls Initiative for Learning And Empowerment (AGILE) ma'ana atakaice kuma shine; Shirin ilmantar da yara mata da kuma koya masu sana'a domin samun daidaito da takwarorin su maza, don samun ingantaccen rayuwa da zamantakewa.
NASARORIN DA SHIRIN AGILE YA FARA SAMU A JIHAR KEBBI
Shirin AGILE a jihar Kebbi sai barka, domin cikin yan watanni da fara aiwatar da shirin, an fara gani a kasa.
A halin yanzu AGILE sun gyara makarantu da dama a fadin jihar Kebbi. Bayan gyara makarantu, shirin ya samar da tallafin makudan kudi ga makarantu da dama domin inganta makarantun da kuma sayo kayayyakin aikin koyarwa.
Ra'ayin jama'ar jihar Kebbi akan shirin AGILE ya nuna gamsuwa da yadda shirin ke aiwatar da aikin sa a jiha tare da kyakkyawan fatar cewa shirin zai share jahilci da talauci a tsakanin yara mata domin samun ingantaccen rayuwa da zamantakewa a cikin al'umma.
A fitowa na gaba, zanyi bayani dalla-dalla akan ayukkan gina ilmi da al'umma da AGILE ke aiwatar wa loko da sakon jihar Kebbi.
----------------------------------
Ahmad Umar
ahmadugamji@gmail.com
07038182929
Post a Comment
0 Comments