HON.HALIMA TA GANA DA DELEGATES A YAURI

HON.HALIMA TA GANA DA DELEGATES A YAURI


A ranar talata 24-may-2022

Hon.Halaima Hassan Tukur wadda aka fi sani da Mai Buje, takai ziyara A ƙananan hukumomin Yauri Shanga da Ngaski.

Hon Takai wannan ziyara ne zuwaga Delegate da kuma ciyamomi domin neman goyon bayansu akan bata dama na tsayawa takara a zaɓe mai zowa jibi idan Allah ya kaimu, wato zaɓen SHARE FAGE na JAM'IYYAR APC (PRIMARY ELECTION)

Ta inda ta samu ganawa da Dukkanin Delegate da excos na  wayannan ƙananan hukumomin.

Da take bayani akan irin taken nata salon na nazartattun yan siyasa. Inda take cewa salon siyasar bana shine :

*ME KA AIKATA BA ME ZAKA AIKATA BA.*
Ta inda tayi amfani da wannan damar ta bayyana ɗimbin ayukkan da ta gabatar zuwaga Al'ummar Yauri, Shanga da Ngaski. Da yake bayani akan irin ayukkan alkhairinda ta gudanar a lokacin Shugabancin ta harma bayan ƙare Shugabancin ta da tayi a baya. Kuma jama'a sunyi na'am sun nuna jindadinsu sosai da kara godewa Hon. Halima Hassan Tukur bisaga jan ƙoƙarinda tayi na kawo musu cigaba mai yawa a wannan nahiya tasu.

*GANI YA KORI JI*
Hon. ta kawo dukkanin ayukkan alkhairinda ta gabatar a rubuce cikin wata haɗaɗɗiyar takarda, 

*ALBISHIR MAI DAƊI ZUWAGA REKU*
Hon. Halima Hassan Tukur tayi albishir mai matuƙar daɗi zuwaga al'ummar Yauri, Shanga da Ngaski na kawo musu wani Babban jirgin ruwa, wanda wannan jirgin yana ɗaukar adadin mutum ɗari da yan kai. Kuma bugu da ƙari jirgine wanda yakeda makewayi da wurin kwana da wurin cin abinci duk acikin sa. Kuma ta tabbatar musu da cewa insha Allah nan zuwa kwana shida wannan jirgin zai ƙara so zuwa garesu.

Daga bisani tayi Alƙawarin cewa insha Allah zata kawo cigaba mai yawa idan Allah yasa ta koma Saman kujerar da take nema ta waƙiltar su a majilalisar tarayya.

Post a Comment

0 Comments