Siyasar Karamar Hukumar Dandi
Mai Laya Kiyayi Mai Zamani (1)
JAM'IYAR APC TA BAYYANA DALILAN DA SUKA SA TA TSAYAR DA DR. MANSUR A MATSAYIN DAN TAKARAN SHUGABAN KARAMAR HUKUMAR DANDI
Bayan jita-jita da kananan maganganu yanzu dai ta tabbata DR. MANSUR Ne ake zance a Dandi kaf; ma'ana shine jam'iyar APC ta tsayar a matsayin dan takara kuma zababen shugaban Karamar Hukumar Dandi In Sha Allah.
WANENE DR. MANSUR ISAH KAMBA?
An haifi Dr. Mansur Isah a garin Kamba, yayi ilmin addinin musulunci da na firamari da na sakandare duk a cikin garin Kamba.
Yayi Diploma da HND da Advanced Diploma da Digiri da Mastas Digiri da digirin digirgir watau PhD duk akan ACCOUNTING. Ya karancin 'Professional courses' da dama Suma duk akan ACCOUNTING.
Abin mamaki duk zurfin sa a ilmin boko, Dr. Mansur bai taba yin aikin Gwamnati ba, ballantana yasan yadda ake satar kudin gwamnati.
Ya fara aikin 'Traveling Agency' a Kamfanin Nazia Airline a shekara 1999 Inda ya rike mukamai da dama har zuwa shekara 2012 Inda ya bude Kamfanin sa mai suna ISMA TRAVEL AND LOGISTICS SERVICES LIMITED, Allah Ya albarkaci wannan kamfani saboda irin dimbin alheri da rufin asirin da ya samu a wannan kasuwancin.
Sabanin halayen wasu na bushasha da almubazzaranci idan sun sami kudi, Dr. Mansur ya kirkiro da gidauniya Mai suna MANSUR ISAH FOUNDATION Inda ya dinga taimakon jama'a musanman matasa da mata a bangarorin rayuwa da dama.
Yawan taimakon sa ne yasa jama'a suka tilassashi shiga siyasa ba don yana bukata ba.
Ya dade yanayiwa siyasa hidima amma sai Zowan Dattijon adalin Gwamna DR. NASIR IDRIS (KAURAN GWANDU, GARKUWAN ZURU, GAMJIN YAURI, JIGON KABI) Yayi tsayin daka cewa sai ya sakawa Dr. Mansur bisa gudumuwar sa ga cigaban jama'a da Kuma jam'iyar APC. Wannan shine sirrin soyayar Mai girma Gwamna da Dr. Mansur. Duk Mai son KAURAN GWANDU Yaso shi to ya dinga Alheri ya kuma guji cin kayan jama'a.
DALILAN DA SUKA SA AKA TSAYAR DA DR. MANSUR
1- Mai girma Gwamna His Excellency Kauran Gwandu da uwar jam'iyar APC sun gamsu da irin taimakon da Dr. Mansur yake ba jama'a da Kuma jam'iyar APC
2- Rahoton Jami'an tsaro ya wanke Dr. Mansur sak, tun daga inda yayi karatu har zuwa inda yayi kasuwancin sa baitaba cin amanar kowa ba.
3- Mai girma Gwamnan His Excellency Gamjin Yauri, da uwar jam'iyar APC sun gamsu da rikon kwarya da Yayi a matsayin Kantoma kamar haka:
a- Bai taba satar kayan palliative ba
b- Bai taba cin Albashin kowa ba
c- Ba a taba bashi kudi don yayi aiki ya cinye su ba
d- Bai taba amshe hilayen mutane ya sayar ba
e- Bai shan Tabar wiwi
Wayannan dililan ne suka kayar da wasu Yan takara, amma cikin ikon Allah Dr. Mansur duk ya tsallake su.
A biyo mu a fitowa na biyu maitaken; MAI LAYA KIYAYI MAI ZAMANI (2) Domin Jin irin ayukkan alheri da Dr. Mansur Isah Kamba ya tsara Yi wa mutanen Dandi idan aka rantsar da shi a matsayin zababen shugaban Karamar Hukumar Dandi In Sha ALLAHU.
__________________________________
ahmadugamji@gmail.com
07038182929
Post a Comment
0 Comments