Shugabancin karamar hukumar Ngaski
Shugabancin karamar hukumar Ngaski
Zaben Kananan Hukumomi Na 2024: MUTANEN KARAMAR HUKUMAR NGASKI SUN YANKE SHAWARAN ZABEN HON. MANIR WARAH BISA GAMSASSUN DALILAI 20.
Yayin da zaben shuwagabanin kananan hukumomi a Jihar Kebbi ke gabatowa, mutanen karamar hukumar Ngaski dake kudancin Jihar Kebbi sun dandale akan hazakin matashin Dan siyasa kuma shugaban riko na karamar hukumar watau Hon. Manir Warah bisa dalilai har guda 20 kamar haka:
1- Kishin ci gaban karamar hukumar Ngaski da mutanen ta. Sun bada misali da daukar matasa aikin sojoji da akayi kwananan, cikin shugabanin kananan hukumomi 21 a Jihar Kebbi Hon. Manir Warah ne Kawai ya ziyarci matasan karamar hukumar sa, ya basu tallafi Kuma ya nemi Alfarma ga masu daukan aikin soja, wanda sanadiyar haka yasa Ngaski ta samu kaso maitsoka da bata taba samuba, ma'ana an daukar masu matasa da dama aikin soja.
2. Shugaba Hon. Maniru yaraba taki zamani (Fertilizer) tareda irin shuka ta shinkafa ga daruruwan manoma
3. Shugaba Hon. Maniru yaraba kayan Sallah (Tufafi) hadi da abincin hidimar Sallah karama ga Marayu da gajiyayyu abinda ba a saba ganiba a siyasar Ngaski
4. Shugaba Hon. Maniru ya kirkiri sabuwar magudana ruwa metsawo ma'auni 215m (meter) domin kare gidaje da sauran dukiyar al'umman Ngaski
5. Shugaba Hon. Maniru yana biyan kudin ma'aikata batareda kowa yarasa sisin kobo ba (salary) bai kuma dakatar da kowa daga aiki ba, asalima idan aka zabeshi zai samarwa mutane da dama aiki
6. Shugaba Hon. Maniru ya tallafawa wasu matasa da jarin kudi domin dogaro dakai
7. Shugaba Hon. Maniru yabada kudi ga daliban Makaranta Bin Sulaiman Tahfizul Qur'an dasukayi saukan karatu a Makaranta (Al-Qur'an)
8. Shugaba Hon. Maniru yakan ziyarci Asibiti domin bada tallafi kudi ga marasa lafiya
9. Shugaba Hon. Maniru ya tallafa a harkan wutan lantarki cikin awanni da ake samu
10. Shugaba Hon. Maniru yaba shuwagabani jam'iyyar APC ta Ngaski local government Shanu alokaci murna Sallah karama a karon farko a tarihin siyasar Ngaski
11. Shugaba Hon. Maniru yana bada kyautar kudi aduk karshen wata ko tsakiya ga Sarakuna, Malamai, Dattijawa, Marayu dama gajiyayu
12. Shugaba Hon. Maniru a harkan lafiya yataka rawar gani sosai da hanyar Samar da magunguna da sauran kayan aiki
13. Shugaba Hon. Maniru yakan ziyarci jami'an tsaro tareda basu tallafi abinci harda kudi kama daga Sojoji, Yan sanda, Jami'an gidan kurkuku, dama saurasu
14. Shugaba Hon. Maniru yabada tallafi kudi da abinci ga al'umma kasar Ngaski
15. Shugaba Hon. Maniru ya sasanta tsakani Jami'an tsaro masu kulada ma'adanai na kasa da jama'an garin Libata
16. Shugaba Hon. Maniru yatallafa wurin samarda ruwa a masallaci juma'a na Yadi
17. Shugaba Hon. Maniru yadau nauyi kayan auren wata baiwar Allah data Muslunta dama saura mutane a Ngaski
18. Shugaba Hon. Maniru ya tallafa makarantu na islamiya da na boko da dama
19. Shugaba Hon. Maniru yabawa shuwagabani jam'iyyar APC na gundumomi goma dake karamar hukumar mulki ta Ngaski kudi dun hidimar Sallah Babba
20. Shugaba Hon. Maniru yabawa Malamai, Sarakuna, Limamai, tareda Imam na kowani gundumomi goma kudi domin yin hidimar Sallah Babba.
Bisa wayannan dalilan yasa mutanen karamar hukumar Ngaski sukace tun ranar Laraba sun gano juma'ar Hon. Maniru zatayi kyawo.
Ma'ana cikin yan'wattani ya aiwatar da wayannan dinbin ayukkan alheri, idan ya sami shekaru a kan kujeran Allah ne kawai yasan irin ayukkan ci gaban da zai kawo karamar hukumar su ta Ngaski; DON HAKA SUNJI, SUN GANI, A 31 ga watan August,2024 sai HON. MANIRU WARAH na Jami'ayar APC, IN SHA ALLAHU
Post a Comment
0 Comments